MACEN DA BA A IYA SAKI 01

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(01)*

        *ADO DA KWALLIYA*

     "Yar uwa mai Albarka ki sani cewa babu yadda za'ayi ace mace tana lazimtar ado da kwalliya cikin rayuwarta face ta Kasan ce mai daraja da kima wajan mai gidanta, hakan tasa farin jakada babba dan Abdullah Muhammadurrasulullahi saw yake cewa "Mummuni bai taba samun wani abu ba mai cike da Alkhairi bayan samun tsoran Allah sama da ya samu mace tagari , wacce idan ya kalleta zata faran ta masa".haka zalika ummuna Aisha ako da yaushe take kwadaitar da mata akan su dage da yin kwalliya da ado dai dai gwargwadon ikonsu. 
   Babu yadda za'ayi ki faran tawa abun qaunarki kina mai nisantar yin ado da kwalliya, haka zalika wata mata mai suna umama yar haris take yiwa 'yarta nasiha ya yin da zata aurar da ita tace "Kada ki bari idon mijinki yakai zuwa gare ki akan abun da zai bakanta masa, kada ki bari ya shinshini wani abu daga gare ki face abu mai kamshi. 
   Haka zalika Abdullahi bn ja'afar lokacin da zai aurar da "yarsa yake mata nasiha akan cewa "ina gargadarki da yin ado, kuma ki sani abu mafi kyawu a ado shine saka kwalli haka zalika abun da yafi saka turare shine yawan wanka". 
  An tambayi wani mutum mai hikima aka ce dashi wace ce kyakykyawar mace? Sai yace "wacce take zuwa ga idon mijinta da hancinsa da zuciyarsa. 
  Babu yadda zuciya, ido ko hanci na mai gidanki su kaunaceki bakya ado da kwalliya, don haka "yar uwata mai daraja Kada ki bari mijinki ya shinshini wani abu daga gareki face kamshi, kada ki bari ya kalli wani abu daga gare ki face kyakykyawa, duk lokacin da kika lazimci aikata hakan tabbas, kece macen da muke wa laqabi da macen da ba'a iya saka, saboda kinfi karfin saki.

*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 02*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏

Post a Comment (0)