KWADAITARWA AKAN YIN SALLAR NAFILA CIKIN DARE(QIYAMUL LAIL).
1-Annabi s.a.w yace:
(Mafi alkhairi da falalar Sallah bayan sallar Farillah,itace Sallar lafiyar cikin Dare).
@رواه مسلم (1163).
2-Manzon Allah s.a.w yace:
(Inayi maku wasiyya akan kuyi riko da Sallar cikin dare,domin Dhabi'ar mutanan kirkice ta wadanda suka zo kafinku,Kuma tana kusantar da ku zuwq ga Ubangijinku,kuma kankarar zunubaice agareku,kuma tana goge laifuka).
@حسنه الألباني في إرواء الغليل (452)
2-Annabi s.a.w yana cewa:
(Lallai acikin aljanna akwai wani kataferan Bene,ana ganin cikinsa daga waje,kuma ana ganin wajansa daga cikinsa,)sai wani Balaraban Kauye yace:
"Na wanene ya Manzon Allah??" Sai yace:
(Na wanda yake:
-Kyautata magana
-Yake ciyar da abinci dan Allah
-Kuma yake azumin Nafila
-kuma ya tashi yake sallar dare lokacin da mutane suke barci).
@حسنه الألباني في صحيح الترمذي
TAYAR DA IYALI DAN YIN SALLAR DARE TARE YANA LADA MAI GIRMA
1-Daga Hindu Bintul Haris daga Ummu Salmata R.A Matar Annabi s.a.w tace:
"Wata rana Annabi s.a.w ya tashi cikin firgici acikin dare yana cewa:
•سُبحانَ اللهِ
SUBHANALLAH
Wani Abune Allah ya saukar na Taskoki,wani abune Allah ya saukar na Fitina Wazai Tayar min da iyalina koda zasuyi Sallar nafila acikin dare,sau da dama mai tufafi anan duniya zai tashi marar tufafi a lahira).
صحيح البخاري ( ٧٠٦٩ ) ].
2-Annabi s.a.w yana cewa:
(Allah ya jikan bawan da ya tashi cikin dare sannan ya tayar da matarsa dan suyi Sallah acikin dare,idan taki tashi sai ya sanya mata ruwa a fuskarta dan ta tashi,kuma Allah ya jikan matar da ta tashi cikin dare sannan ya tayar da mijinta dan suyi Sallah acikin dare,idan yaki tashi sai ta sanya masa ruwa a fuskarta dan ya tashi)
@صححه الألباني في
[📚 صحيح الجامع ( ٣٤٩٤ ) ].
3- 2-Annabi s.a.w yana cewa:
(Idan Namiji ya tashi cikin dare,sannan ya tada matarsa sukayi Sallar raka'a biyu na nafila acikin dare,za'a rubuta su cikin bayin Allah masu ambaton Allah mai yawa).
@صححه الألباني في صحيح ابن ماجة ( ١١٠٦ ) ].
Awata ruwayar yazo da wannan Lafizin:
(( مَن استَيقظَ مِن اللَّيلِ وأيقظَ امرأتَهُ فصلَّيا ركعتَينِ جميعًا ، كُتِبا مِن الذَّاكرينَ اللَّهَ كثيرًا والذَّاكراتِ )) .
@صححه الالباني في صحيح أبي داود ( ١٤٥١ ) ].
Allah ya jikin wanda ya yada wannan alkhairi ga Al'umma.
Ya kuma sanya mu cikin bayinsa masu yawan ibadar dare da kyakkyawar niyya da Ikhlasy.