LABARIN WASU SAMARI BIYU DA WATA BUDURWA

LABARIN WASU SAMARI BIYU DA WATA BUDURWA


Wasu samari biyu Abu da Salisu na tafiya akan hanya, sai suka zo wucewa ta gaban wani gida mai bene. Wata kyakyawar budurwa ta leko daga window tana masu murmushi.

ABU: kai Salisu dubi wata kyakyawar yarinya can tana mana murmushi.
SALISU: Hmm kyale ta kawai, zo mu tafi.
Har sunyi gaba sai Abu ya kara waigowa, sai ta yi masa alamun zo da hannu.
ABU: Salisu tana kirana fa
SALISU: ka kyale ta nace, zo mu tafi.
ABU: kai ko anya ba bakin ciki kake min ba. Gaskiya sai naje.

Sai Abu ya nufi gidansu yarinya, ta shigar dashi falo suka gaisa, ta kawo masa abinci da abinsha. Kafin ya fara cin komai sai suka ji mota ta tsaya. Budurwar ta leka window tace “ga mijina ya dawo”. Abu ya tashi a tsorace yana neman hanyar fita sai yarinyar tace “zo kaga dauki kayan nan ka fara guga, in ya shigo zance mai guga ne na kira”. Abu ya kwashi tulin kaya ya cigaba da guga, ya kwashe ranar gaba daya yana guga kaya sunki karewa kuma mijin bai fita ba.
Da safe sai Abu da Salisu suka hadu a hanya.
ABU: hmm Salisu kasan jiya wuni nayi ina guga a gidansu yarinyar nan kuwa.
SALISI: ba nace maka kar kaje ba, duk kayan nan daka gani ni na wankesu shekaranjiya.
Post a Comment (0)