LABARIN WANI ƊAN BALA DA AKU

LABARIN WANI ƊAN BALA DA AKU


Wataran DAN BALA ya sai wata aku tun tana yarinya ya kiwata ta ta girma saboda yawan yawo da yake da ita da shiga jamma a da yake da ita yasa ta koyi shegen surutu. Wataran wani abokinsa yadawo daga saudiyya sai yaga DAN BALA da akun nan
kawai sai ya bashi shawara ya kaita saudiyya ya saida ita dan zatai daraja agun larabawa DAN BALA ya dau shawara sai dai
kuma ba shi da ko sisi sai gidan sa kwaya 1. Akai shawara akasai da gida akace inya dawo zai sai babban gida haka a kai kuwa
bayan ansai da gida DAN BALA ya kama aku suka tafi saudiyya aku tana ta surutu har aka sauka a JIDDAH sukaje suka huta.
Washe gari sai kasuwa ana zuwa kasuwa larabawa suka zagaye DAN BALA yasu da aku daga nigeria dan bala sai yanga yake
sai wani balarabe yace zai saya amman sai yaji yadda take magana DAN BALA ya juya gun aku yayi yayi magana aku tai shiru abu kamar wasa haka akai tayi amman aku kotace uffan taki magana har aka kwana 13 amman aku taki magana ga lokacin komawa gida Nigeria yayi haka DAN BALA ya hakura suka dawo gida nigeria saukar suke da wuya a airport sai aku tai wani dogon numfashi tace mai gida amman fa munsha wahala. Shiko DAN BALA budar bakinsa sai cewa yayi ai bakiga wahala bama saina FIGEKI DA RANKI.
Post a Comment (0)