MACEN DA BA A IYA SAKI 02



*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(02)*
        
*NISANTAR CUTAR DA MIJINKI*

   "Yar uwa mai daraja ki sani cewa samun miji nagari ni'ima ce daga cikin ni'imomin ubangiji gare ki, nawa ne daga cikin abokan karatunki, qawayenki, "yan uwanki basu samu wannan ni'imar ba, suna kallonki kamar wata sarauniya saboda baiwar miji nagari da kika samu, wasu na roqon su samu ko da wanda bai kai naki ba, don haka 'yar uwa mai daraja ki kiyaye cutar da mai gidanki domin shine jin da dinki duniya da lahira.  
Farin jaka babba dan Abdullahi Muhammadurrasulullahi saw yana tsoratar da mace akan cutar da miji yake cewa "Babu wata mata da zata cutar da mijinta anan gidan duniya, face matarsa daga cikin matan Aljannah tace :kada ki cutar dashi Allah ya tsine miki, yanzu dai yana wajanki ya yi daf yabarki ya dawo waje na ". Haka zalika Annabi dawud (saw) yana cewa :mace mai cutar da mijinta kamar kaya mai nauyi ne akan dattijo mai yawan shekaru.". Haka zalika luqmanul hakim yana cewa dan sa "ya kai da na ka guji muguwar mace, domin zata tsufar da kai kafin lokacin tsufar ka, ka guji miyagun mata domin kwata-kwata basa kira zuwa ga Alkhairi".
    don haka "yar uwata mai daraja ki guji aikata abun da zai ba tawa mai gidan ki rai ta ko wacce fuska domin shine Aljannarki kuma shine wutarki.
 Daga lokacin da kika kasance kina mai nisantar aikata hakan tabbas kece macen da muke wa laqabi da macen da ba'a saki domin babu yadda za'ayi mai gidanki ya iya rabuwa dake. 


*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 03*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)