MACEN DA BA A IYA SAKI 03



*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(03)*

   *KI YA WAITA MURMUSHI GA MIJINKI*

   "Yar uwata mai daraja ki sani cewa murmushi ala mace da ke baiyana taushin zuciya tare da qauna, ki sanya murmushi akan labbanki ako da yaushe domin mai gidan ki ya gani a duk lokacin fuskarsa ta kai zuwa gare ki, tabbas aikata hakan zai janyo miki lada guda biyu wajan ubangijin ki ladan murmushi da ladan faran ta zuciyar mai gida. 
   An tambayi wasu maza je :wane abune mafi faran ta muku rai daga wajan matayenku? Sai daya yace kyakykyawar fuskarta mai walwali ya yin da take murmushi. 
   Dayan kuma sai yace : dukkanin wata wahala da na shawo tana tafiya ya yin da mata ta take fuskanta ta cikin murmushi. 
   Sai na qarshe yace ai murmushin mace ga mai gidan ta shine rabin jin dadin rayuwa, rabi kuma yana cikin hutun da zai yi a cikin gida. 
   Wani bawan Allah talaka mai sana'ar farauta ya kasance tare da matarsa cikin jin dadi da farin ciki,daga cikin dabi'arta duk lokacin da zai tafi farauta tana bin sa har qofa tare da murmushi haka zalika idan ya dawo da yamma tana fuskantarsa ta cikin tarairaya tare da murmushi, yana matuqar qaunar wannan murmushin nata, shi da kansa yake nema daga gareta ta kasance cikin murmushi ako wane lokaci, ya yin da mijin nata ya mutu, sai tayi Alqawarin cewa baza ta sake yin murmushi ba bayan sa, haka ta rayu har qarshen rayuwarta tana mai nisantar yin murmushi. 
     'Yar uwa mai daraja ki sani tabbas murmushi yana daga cikin abun da zaki mallake zuciyar mai gidanki, tabbas kina lazimtar murmushi acikin gidan mijinki ki zama wacce muke wa laqabi da macen da ba'a iya saki. 


*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 04*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)