MACEN DA BA A IYA SAKI 04

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 


🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(04)*
         
                 *GIRKI*

   "Yar uwa mai daraja ki sani cewa tabbatarki cikin gidan mijinki, shine abu mafi soyuwa da qauna wajen mahaifanki, da duk wanda yake miki fatan Alkhairi a wannan rayuwar. 
   Ya "yar uwa mai Albarka yana daga cikin abubuwan da zaki mallake zuciyar mai gidan ki tare da kwantar masa da hankali ya yin da yake cikin fushi shi ne kwarewa tare da gogewa wajan kala-kala da nau'i-nau'i na abinci, ki zama "yar birni wayaiya wajan abun da ya shafi girki, kuma ki kula sosai daga cikin nau'i-nau'i na abinci , wanne abun qaunar ki yafi so da qauna, ya yin da kika fahimci hakan yi qoqari wajan sarrafa wannan nau'in abincin zuwa nau'i kala-kala, yanzu duniya an waye kina gida zaki iya koyan nau'i kan abinci kala-kala, tabbas "yar uwa mai Albarka aikata hakan zai qara janyo miki soyayya wajan mai gidan ki, shi da kansa zai dunga gudun abun da zai bata miki rai, haka zalika kada ka sake ki barsa yaci abinci shi kadai ba tare da kina kusa dashi, domin lokacin da yake ci a lokacin zai baki saka makon da kika samu, ko da bai fada ba fuskarsa zata baki, amma nisantarsa ya yin da zai ci abinci na iya jawo miki rasa wannan saka makon, haka zalika bazai taba zuwa wani waje yaci abinci ba saboda yasan yana da kyakykyawan abinci agida, idan ya kasance dole sai yaci bazai taba bari ya cika cikinsa ba maqil. 
   "Yar uwa mai daraja ki zamo wacce kullum mai gidanta zai dunga tunanin yau kuma wane nau'in abinci abar qaunarsa ta tana dar masa, tabbas "yar uwata idan ki ka siffantu da wannan siffar kece wacce mukewa laqabi da macen da ba'a iya saka.

*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 05*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)