MACEN DA BA A IYA SAKI 05

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 


🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(05)*
                   
*YIWA MAI GIDA KYAUTA*

    "Yar uwa mai Albarka shin kin taba yiwa mijinki kyauta kuwa? Kin taba siyan abu da kudinki domin mai gidan ki kuwa? Matso kusa ga wani sirri wanda bana buqatar komai a wajanki face Addu'a, "yar uwata mai daraja me kike buqata ne a gidan duniya da wuce Kasan cewa tare da mai gidan ki cikin aminci da kwanciyar hankali, daya daga cikin hanyoyin da zaki bi wajan samun wannan kwanciyar hankalin shine yiwa mai gidan ki kyauta. 
   Zaki iya cewa ta ya ya? Gaskiya ne ita kyauta ba yawan abun da aka bayar ake kalli ba ko kankantarsa, ana kallon wanda ya yi ta,la'alla kina adashi ko kuma kina sana'a ko kuma kina dan samu daga cikin abun da yake baki na cefane, da wannan abun da kike ta rawa zaki yi amfani da shi wajan gwangwaje abun qaunar ki ta hanyar siya masa wani abu wanda zai yi amfani dashi kamar agogo, takalmi, hula, tabarau, da makamantansu ki yi masa kyauta dashi, aikata hakan zai janyo miki riba guda biyu daya qara samun soyayya daya kuma zai qara dagewa wajan kyauta ta miki domin yasan tabbas ko da ba shi dashi zaki iya tai maka masa. 
   Bari na baki wani labari wata rana na bawa wasu "yan uwa mata shawara akan yiwa mazaje kyauta daya daga cikin su ta gwada kuma ta samun wadannan abubuwan da na lissafa tace na sai masa takalmi ne, lokacin da ta basa kasa cewa komai ya yi saboda mamaki, tace takalmin bai wuce 2000 ba amma sai da ya yi mata siyayyar ba a irin lokacin da ya saba yake mata siyayya ba kuma ta linlinka abun da ta yi masa ga kuma qarin samun kulawa daga garesa. 
    "Yar uwata mai Albarka da zaki jarraba wannan abun da nake faba tabbas zaki zama daya daga cikin matan da muke wa laqabi da cewa matan da ba'a iya saka.

*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 06*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)