WA ZAN AURA?

*👫 WA ZAN AURA?!*


Mai Tarin ilimin addini ko Mai kyawawan Hali?

Haqiqa ilimin addini wani ma'auni ne da akan yi amfani da shi wajen auna nagartar mutum, sai dai haqiqa a wannan zamani da muke ciki al'amarin ya sauya, za ka samu mutum da tarin ilimi amma ba shi da nagarta. 

Da za mu yi waiwaye zuwa tarihin da muka tsinta daga magabatanmu da hasashen mu zuwa yadda suka wanzar da rayuwarsu, za mu samu cewa haqiqa a wannan lokacin sun yi fama da qarancin ilimi, jahilci ya yawaita, kai hatta wa'azi sai dai a isar da shi ta hanyar *tatsuniya* (fable), amma duk da irin wannan rashin sani da suka yi fama da su tarbiyyarsu ta zarce tamu nesa ba kusa ba, mutane ne masu kunya mazansu da matansu, suna tsoron aikata dukkan alfasha saboda gujewa abin kunya ba don sun san haqqin Allah a kan shi ba, suna gudun Qarya, yaudara, fasiqanci, cuta, ga Kuma kokarin qarfafa zumunci da 'yan uwa na kusa da na nesa. Wannan ke nuna cewa akan samu mutum da tarbiyya koda ba shi da tarin ilimin addini. 
.

Wannan shi ya sa a wajen za6en abokin rayuwar aure, Annabi (ﷺ) ya yi mana nuni da mu za6i mutum *Mai addini da kyawawan ďabi'u.* Da farko dai mutum *mai addini* dole ne ya kasance musulmi, Kuma za a same shi da kai wa matuqa wajen kiyaye dokokin Allah, abin da Allah da manzonSa (ﷺ) suka yi umarni shi yake yi, abin da Kuma suka yi hani yana qaurace masa gwargwadon iko, sannan yana kokarin yin umarni da kyakkyawa da yin hani ga mummuna. Shi kuwa *kyawawan ďabi'u* ya danganci kyautatawarsa ga iyayensa, 'yan uwansa, makwabtansa tare da alaqarsa da sauran jama'a, ba a samun shi da raina mutane, yawan faďa ko yawo da zancen wani ko annamimanci, sannan ba ya mu'amala da mutanen banza. Waďannan siffofi guda biyu su ne ake dubawa yayin za6en miji/mata ba wai tarin iliminsa ba. 

Ba ina cewa auren mai tarin ilimi aibu bane, idan ka yi dace ka samu mutum Mai ilimi, Mai addini, mai tarbiyya, kun ga haske bisa haske kenan (light upon light). Alal haqiqa Kuma wauta ne auren jahili, domin jahili ba abokin zama bane, abin da dai nake nuni shi ne kada ka ce sai wadda/wanda ya yi zurfi a ilimi, amma ko hizfi ďaya mutum ya iya daga Alqur'ani, ya san yadda zai bauta wa Ubangijinsa ai ya wuce jahili. 

Ina mamaki idan na ji wani/wata suna cewa su ai sai Mahaddaciyar Alqur'ani, ko sai wadda ta kware a larabci, ko sai mai ilimi kaza da kaza, wannan rashin ganewa ne, domin tarin iliminta ba shi ke nuna tarbiyyarta ba, kana ina kafirai ma suke haddace Alqur'ani? A yanzu sai ka samu mutumin da babu hizfi biyar na Alqur'ani a kanshi amma ya fi kyautata mu'amala da mutane fiye da wani mahaddacin Alqur'anin, a wannan zamani za ka iya samun mutum mahaddacin Alqur'ani amma mushriki ne, ka samu mahaddacin Alqur'ani Kuma ya san hadisai amma yana zina, ka samu mutum ya san dokokin Allah amma yana qetare su, so Nawa mace za ta auri mai ilimin addinin amma ta yi ta shan wuya a gidansa wani ma har da duka? Sau nawa miji zai auri mace mai ilimin addini amma ya kasa bambance ta da wadda ko hanyar islamiyya ba ta sani ba? Don haka ka natsu sosai wajen za6en uwa/uba wa 'ya'yanka/'ya'yanki. 
.

Don haka idan mutum ya zo neman aurenki, abin da aka ce a duba shi ne addininsa da kyawawan ďabi'unsa, ba wai ki ce sai wanda ya fi ki ilimi ba d.s. Tunda kin yi karatu kin ga ke makaranta ce a gidansa, Kuma shi ba zai hana ki ci gaba da neman ilimi ba. 
.

Shawara ☺ 

Domin samun abokin zama nagari, ka fara zama nagari, domin Allah Ya ce: *Nagartattun maza na Nagartattun matane”.* Sannan sai ki ci gaba da rokon Allah za6i nagari.

Allah Ta'āla Ya haďa mu da abokan zama solihai. 

.

✍🏿Ayyub Musa Giwa.
*▪️ANSAR.*
*25/04/2019.*

*📚Irshadul ummah WhatsApp.*
Post a Comment (0)