Masu Gemu Ma Ya Sa Su Bacci Bare Jariri?
Shehu Jaha
Wata Rana Matar Shehu ta zo wajensa cikin dare hankalinta, atashe, tana cewa da shi: Na Rasa abin da yasami yaron nan; Babu abin da yakeyi ban da Kuka akoda yaushe, kuma na yi masa irin dukabin da zan iya don ya yi bacci, amma abu ya gagara! ka yi masa wani dan kokari mana, ko ya samu ya yi bacci, ko dai ka yi masa abin da kaga ya fi dacewa, ni duk hannayena sun gaji da daukar sa da jijjiga shi.
Sai ya ce da ita:
Saboda me kika rude haka?
Dauki wannan littafin ki buda shi, ki ajiye a Gabansa. Sai matar ta fusata tana fada, tana cewa: Yanzu wasa za ka yi mini game da wannan lamari?
Haka kuma za ka yi mini, bayan ka auro ni tun da kuruciyata, ka gama biyan bukatarka da ni, ka bar ni cikin yunwa da tsumma, alhali ina ta faman yi maka hidima ba-dare-ba-rana, kuma wannan yaro danka ne, ba agola ba?
Saboda me za ka Rinka wasa da hankalina a Kowane lokaci?
Sai Shehu ya amsa mata da cewa: Haba Hajiya? Ai kuwa ina yin bakin kokarina, wajen kyautata Rayuwarki, saboda me za ki rinka yi mini irin Wannan magana mai zafi, kina tayar mini da Hankali?
Sai matar ta rage karfin muryarta, Sannan (afusace) taci gaba da cewa: To Wannan littafin na mene ne, kuma wace fa’ida Za’a samu a cikinsa?
Sai ya ce: Kwantar da hankalinki, wannan littafin “KADURI” ke nan, (Wani littafine, Mara ma’ana da ya kunshi Bayanai na rashin kan gado) Wanda duk lokacin dana karanta shi ga Almajirai a Masallaci, sai Bacci ya kwashe su, wasu ma har kiji suna Minshari. To idan kuwa har zai iya sanya bacci Ya kwashe magidanta masu gemu, kamar Wadan da aka yiwa sihiri saboda tasirinsa,
Mezai hana ya sanya jariri ya yi bacci kamar ya Shaki banju?
Kunjifa Wata Hikayar Shehu?