SUNA: BARRATU DA BARA'ATU
Tambaya:--
ina yiwa malam fatan alheri. Mun samu tambaya kamar haka:
Dan allah sunana bara'atu kuma naji wai ance fasarar sunan bashi da kyau,dan allah menene fasarar sa kuma zan iya cigaba da amsawa ko saidai a canja. Nagode.
Amsa:--
1) Bai kamata a saka suna "Barratu" (matar kirki) ba, haka ma kowace suna mai nuna tsarkaka.
[UMDATUL QA'RY; 22/320, ZA'DUL MA-AD; 2/306]
.
.
2) Annabi ya canza wa mata sunaye daga Barratu.
[SAHI'HU MUSLIM; 2140,
SILSILATUS SAHI'HA; 212, 2156,
SAHI'HU ABI DA'WUD; 1347]
.
.
3) "Bara'atu" sunan Surar al-Qur'ani ce, an saukar da ita ne don bayanin "barranta Allah da ManzonSa daga kafirai". A na hana riķon sunayen surori a matsayin suna ga Dan Adam.
[TUHFATUL MAWDUD; 127, AL-MU'UJAMU MANA'HIL LAFZIYYA; 565]
.
.
Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a bibiye mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram:---- https://t.me/Miftahulilm2
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248