MUSIBA DA BALA'I

MUSIBA DA BALA'I


Tambaya

Allah qara ma malam imani m da lafiya. 

Daga qasar Niger ne. Munajin dadın karatuttukan malam. Allah ya biya. 

Dan Allah malam inada tambay. 

1. Yaya bawa zai iya bambata jarabta da kuma uquwba dake zo masa daga Allah?

2. Wasu dabi'u ne ke sa bawa ya gane cewa yayi haquri kuma ya yarda da jarabtar da Allah ya masa.

Amsa:- 

1) Idan a na samun fitina kuma akwai zunubin da a ka ķi bari to a dalilinsa ne, shi ne musiba. Idan ba a tuna naciya ga wani zunubi ba to bala'i ne (ibtila'i), jarabawar imani mai alamar Soyayyyar Allah Mađaukaki.

 [SILSILATUS SAHI'HA; 146]
.
.
2) Kowace damuwa da musiba ta samu musulmi, ya na samun lada a kanta, idan ya yi hakuri da fatar samun ladar. 
[SILSILATUS SAHI'HA; 2503]
.
.
3) Kamar yanda mai samun ni'ima ya ke samun lada a kan godiya haka ma mai rasata ya ke samun ladar hakuri.

 [MUSLIM; 2999, ZA'DUL MA'AD; 4/189]
.
.
4) Allah Madaukaki Ya na ba mai hakuri lada fiye da na kowane yanayi, ladar mai hakuri ba ta da adadi. [AT-TAS'HI'LU LI-ULU'MIL QUR'AN; 2/266]
.
.
5) Annabi (صَÙ„َّÙ‰ اللَّÙ‡ُ عَÙ„َÙŠْÙ‡ِ ÙˆَآلِÙ‡ِ ÙˆَسَÙ„َّÙ…َ) ya ce; INA MAMAKIN MUMINI; IDAN MUSIBA TA SAME SHI SAI YA YI FATAR SAMUN LADA DA KUMA HAKURI, IDAN ALHAIRI NE SAI YA YABI ALLAH DA KUMA GODIYA GARESHI.

 [Sahi'hul Ja'mi-i; 3986]
.
.

Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a bibiye mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram:---- https://t.me/Miftahulilm2

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)