Maigida abin fa akwai zafi! 🤔
Shekaru aru-aru kana tare da Uwar gidanka, ga zuriyya ka samu tare da ita, amma lokaci guda ka yi sabuwar amarya ka fara juya ma Uwargida da 'ya'yanta baya. Menene zai hana su ďauke ta a matsayin kishiya? Shin a haka Kake tunanin yaranka za su dai-daita matsayinta da na mahaifiyarsu?
Kashi 65% a cikin ďari na matsalolin da suke faruwa a cikin gidaje tsakanin mata da 'ya'yan abokan zama (kishiyoyi) laifin Mazaje ne. A kan me don ka kawo sabuwar amarya za ka fara canja mu'amalolinka da tsoffin matanka, ko ka dinga fifita 'ya'yan amarya a kan nasu?
'Dan uwa ka sani fa ita ma tsohuwar matar taka a baya ka auro ta ne da quruciyarta, duk wani sauyi da aka samu kai ma sila ne kuma a gidanka ta same su, wahalar ďaukar ciki, haihuwa, yi maka hidima, kula da yara. Etc duk su suka canja mata kamanni, amma wai har kana da wani za6i na ka fara janye jiki daga gare ta saboda yanzu ta tsufa ko? Mai yiyuwa ta aure ka tun ba ka da wadata, duk wani shige-da-fice da wahalhalu tare kuka sha, amma yanzu Ka samu rufin asiri tunaninka ya fara sauyawa.
A gaskiya matukar muna neman zaman lafiya a cikin gidajenmu, to wajibi ne mu fara tsayar da adalci tsakanin matanmu da yaransu.
Akwai sunnoni dayawa waďanda za ka yi koyi da su, qarin aure ba shi ne kaďai sunnah ba ďan uwa! Ba a shar'anta hakan a kanka ba face sai za ka iya yin adalci. Don haka kada wata ta zo tashi ďaya ta sa ka juyawa iyalanka waďanda kuka daďe kuna fafatawa da rayuwa tare cikin daďi da qunci. Allah Ta'āla Ya sa mu dace.
*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
(Ansar).
*24/04/2019.*
*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*