SHIN AKWAI WATA KEBANTACCIYAR ADDU’A DA AKE WA IYAYE DA SUKA RASU?
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalama alaikum, ina da tambaya kamar haka: Wace addu’a ake wa iyaye mamata a kowace sallah?
:
*AMSA*👇
:
Ba wata katamaimiyar addu'a da aka ware aka ce dole ita ake so a yi wa iyaye mamata idan za a yi sallah, duk wata addu'a halastacciya da ake roqon Allah da ita ga mamata za a iya yin ta da nufin Allah ya gafarta wa iyaye.
Ya tabbata a hadisin da Imamu Muslim ya ruwaito cewa; Aufu bin Malik ya ce:
Annabi s.a.w ya yi wa wata gawa sallar jana'iza sai ya ji addu'ar da Annabi s.a.w yake yi ita ce:
اللهُمَّ اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، وَاعْفُ عَنْهُ وَعَافِهِ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِمَاءٍ وَثَلْجٍ وَبَرَدٍ، وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، وَأَبْدِلْهُ دَارًا خَيْرًا مِنْ دَارِهِ، وَأَهْلًا خَيْرًا مِنْ أَهْلِهِ، وَزَوْجًا خَيْرًا مِنْ زَوْجِهِ، وَقِهِ فِتْنَةَ الْقَبْرِ وَعَذَابَ النَّارِ.
Ma'ana:
Ya Allah ka gafarta masa, ka yi masa rahama, ka kiyaye shi, ka yafe masa, ka karrama masaukinsa, ka yalwata mashigarsa, ka wanke shi da ruwa, da ruwan qanqara, da ruwan sanyi, ka tsaftace shi daga kurakurai, kamar yadda ake tsaftace farin tufafi daga datti, ka canja masa wani gida da ya fi gidansa, da iyalan da suka fi iyalansa, da matar da ta fi matarsa, ka shigar da shi Aljannah, ka tsare shi daga azabar qabari, da azabar wuta. Muslim 963.
Wannan addu'a ta kasance Manzon Allah s.a.w yana yi wa mamaci idan ya zo yi masa sallar jana'iza. Don haka ya halasta a ci gaba da yi wa mamaci wannan addu'ar da makamantanta ko da bayan yi wa mamaci Sallah ne.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ