BANZA TA KORI WOFI

Magana Jarice Ta Alhaji Abubakar Imam.


BANZA TA KORI WOFI

Wata shekara akayi tsananin yunwa a wani gari, har abinci ya zama ba mai ganinsa sai mai dalili. Talakawa da matsiyata ba su da wani abinci sai rogo, rogon ma bai wadata ba. Saboda haka wadanda basu da ko dalilin samun rogon sai suka rika zuwa gonakin rogo da tsakad dare suna satowa.

Ana nan cikin wannan hali, sai wadansu mutum uku suka yi shawarar su tafi gonar madaki su sato rogo. Suka dauki kwanduna, da dare ya raba suka nufi can. Daya daga cikinsu ana kiransa kodago-a-taka-a-karye, guda kuma an ace masa kadan-mai-ban-haushi, daya kuwa sunansa Kazunzumi-a-ganka-raina. Da shigarsu sai suka yi wa juna rada suka ce ya fi kyau su ci tukun, sai sun koshi sa'an nan su diba, gobe su kai kasuwa su sayar. Saboda haka suka suka debo, suka sami wuri suka zauna suna ci. Kodago ya dubi Saura, ya ce, "Kai, ai ko rogon mutumin nan duk zaqo ne."

Kadan ya ce, "Haba, ai zakin ba Magana a keyi ba, in ka sa baki sai ka ji kamar sukar."

Kazunzumi ya ce, "Ai Allah ya buda mana kofar arziki." Tun suna rada har dadi ya sa suka koma magana sosai, kamar suna cikin gidajensu. Da suka koshi suka yi ta tuga suna cika kwanduna.

Kasan dare in yayi tsaka, da anyi 'yar Magana ko da sannu sannu ce, sai ka ji ta da nisa. Saboda haka wadansu 'yan gadi suka jiyo su, suka lababo, suka tasam musu suna cewa, "Kada su kai! Biyo nan, harbar su! Kowa ka gani, kashe shi!" sai suka yi ta bara da ka, suna harba kibiya cul cul.

Wadannan 'yan Gadin wadansu sakarkarun kauyawa ne, sabon shiga. Da jin yadda suka tasam ma barayin nan da hauka haka, ka san gaulaye ne, tashin kauye. Ka san in da 'yan gadin ne na sosai, Allah ya ba ka nasara, sai su lababo da yake ana duhu, su kama su a hannu ba su sani ba. To, ka ga yadda suka bata al'amarin.

Ko da barayin nan suka ji haka fa, sai suka kwashe 'yan kayansu suka runtuma da gudu. 'yan gadi kuma suka dafo su suna cewa, "Kada su kai!" ko da yake ana duhu, har ba mai ganin kowa, duk da haka 'yan Gadin nan na ta kurari, suna bin motsin barayin. Barayin nan suka yi ta gudu kamar ransu zai fita.

Suna cikin gudu dai, sai kodago yayi wa saura rada ya ace, "Kai, ni fa na gaji, ya kamata mu yar da kwandunan rogon nan, mu yi ta kammu."

Kadan ya ce, "Ni ma dai abin da na ke shiri in gaya muku kenan."

Da kazunzumi ya ji haka, sai ya ce, "Kada ku yi saurin karaya. Ku dai dan jure kadan, ku ga tawa dabarar." Sai ya fadi rica, ya ce, "wayyo Allah, ya kasha ni! Ashe, harbin nan da na ce anyi mini, sai yanxu dafin ya narke. Ku ji kaina, "Yan uwa, ku yi mini rai." Ya rada wa sauran abin da za su ce.

Sai suka ce, "Tashi don Allah, mu isa gida, watakila ka sami makari, in ka sha ka amaye shi."

Kazunzumi ya ce, "Ni tawa ta kare, Ina maganar tashi?"

Kodago yace, "Lallabo dai, in fa ka mutu ai lalle mu je Gidan sarki da su, su gaya masa dalilin da ya sa suka kasha ka, don mun debi saiwar rogo zamu ci, kada mu mutu da yunwa."

Kazunzumi ya marairaice y ace, "To, mu tafi in gani, in na iya."

Ko da barayin nan suka ji wannan makircin, sai suka qara mai. Da 'yan Gadin nan suka ji haka, sai guda ya dubi dan uwan, y ace, "Ka ji abin da suka fadi?"

Dan uwan ya ce, "Ai na ji." Shi kuma ya dubi na ukun, ya ce, "Kai ka ji abin da suka ce?"

Na ukun kuma ya ce, "Na ji mana, ai kome ya same su halas ne. Mu matsa, ko sun yar da abin da suka sato, mu gani. "Suka dai yi ta bin su.

Da kazunzumi ya ji suna tafe sai ya sake faduwa, ya ce, "Wayyo, ni kaina! Da dai na ce ko zan kokarta in kai gida, don in sami inda za a lura da ni, kada in kumbura kafin safe. Amman na ji dafin ya ci karfina. Ku ku yi ta kanku, ku kyale ni, ashe da ma kasa ke kirana. In kun isa ku ba mata ta da iyalina hakuri, su tuna duka mai rai mamaci ne."

Da 'yan Gadi suka ji haka, sai suka cirje, suna saurare. Ya sake cewa, "Ku lura da wasicin da zan yi. Ku shaida na ce a ba da sakadar sule talatin da ga cikin kudina da na bari. Kuma ku na baku amanar 'ya 'yana, ku lura da su da kyau, kada su sangarce, Ni tawa ta kare." Ya yi Kalmar shahada. Da 'yan gadin nan suka ji haka sai wannan ya dubi wannan, wannan ya dubi wannan.

Kodago da kadan kuwa sai suka yi ta tafa hannu, suna salami, suna cewa, "Kada ka ga kamar ka yi mutuwar kare, ka ji. Yadda aka kasha ka duk wanda ya yiwo harbin nan ta same ka, shi ma sai sarki yasa an tsire shi, in gari ya waye. Ai cewa aka yi su kama barayi, ba a ce musu su kashe ba. Duk mu tsaya, in ya so in zasu kashe mu ne su kasha mu duka, tun da dai suka raba mu da dan uwanmu. In ko suka kashe mu, ai lalle su ma a kashe su, don mu mu ma musulmi ne, ba kafirai ba."

Da'yan gadin nan suka ji haka fa, sai suka yi tsammani sun kasha mutumin nan ne. Saboda haka suka fara shawarar su gudu, kada a gansu. Suna cikin shawarar inda za su bi, sai suka ji barawon nan na kwance, ya fara kakarin mutuwa, yana shakuwa kikaf kikaf. Can sai ya ja wani kakari mai karfi, yayi shiru. Sauran barayin suka buga salati baki daya, suka ce, "Ya cika."

Ko da 'Yan Gadi suka ji haka, ba su tsaya su gama shawarwarinsu ba, sai kowa ya ce in ba ka yi ba ni wuri. Kazunzumi da jin tif tif tif na 'Yan gadi suna gudu, sai ya tashi ya shiga gaba, sauran na biye har gida.

Da zuwa suka sami ruwa mai sanyi, suka kyankyama. Ka san na gaya maka Kafin su debo rogon nan sai da suka ci daya daga cikinsu tukuna. Abinka da kayan zalunci, ko da suka sha ruwan nan sai danyen rogon nan da suka ci ya taso, ya murde su, kowane yayi ta murde-murde abinsa, yana nishi. Kafin assalatu cikunansu suka haye tim, sai amai sai zawo, gari bai waye ba, sai da duka suka hauri arewa.

Da safe da ka tarad da su kowane cikin nan ya kumbura kamar salka. Gasu kace-kace cikin amai da zawo. Rogo na fita har ta hanci. Aka duba sako aka ga kwanduna cike da danyen rogo, sai aka hakikance danyen rogo suka yi wa cin yunwa, ya halaka su. Aka yi 'yan koke-koke, aka yi musu jana'iza, aka kare. Garin nan fa ya waye, 'yan gadin nan ba su san wannan abin ya auku ba. Da suka gamu da hantsi sai guda yace, "Shin wa ku ke tsammani ya harbi mutumin nan ne na jiya? Ni dai na tabbata bani ba ne."

 Na biyu yace, "Balle fa ni da na ke biye da ku daga baya."

Na uku ya dubi na fari, ya ce, "Amma ko da ku ke neman ku maka mini laifi, ai ku kuka ce in harba."

Na fari ya ce, "I, gaskiya ne, amma ai kai ka san abin da na ke nufi. Ka harba ta ketare kansa, ba ta same shi ba."

Na uku yace, "Ni ma tsammani na ke koli na harba ta. Ina mamakin yadda ta same shi. Kaddara dai ce ta tarad da ajali kusa."

 Sauran suka ce. "Gaskiya ne, sai dai mu yi kurum, kada mu tona kammu."

Daga ran nan duk sa'ad da biyu daga cikinsu suka gamu sai su ta da tadin, su rika kokarin su lika wa wanda ba ya nan laifin. Suka zauna kan hakanan dari dari har iyakar ransu, suna tsammani a gane su yau, a gane su gobe, ba su ji Magana ba. Suna son su tambaya. Suna jin tsoro kada son iyawa ta tona su.

Musa ya ce. "Wadannan 'Yan Gadi sun kuwa isa sakarkaru." Aku yace, "Suma ai suna da hankali bisa ga wani bahaushe wanda ya tafi fatauci cikin kasar yarbawa."

Musa yace, "Har ya fi wadannan sakarci? Haba, wanda ya fi wadannan sakarci ai sai yanka."

Aku yace, "Bari ka ji gogan naka, ka san ko cikin Hausawa akwai Yausawa."
Post a Comment (0)