⚡FA'IDAH⚡04
Ko yana tayar maka da hankali idan ka ko ki ka tuna cewa akwai wata rana da za'a baka ko a baki littafin ayyukan ka ko kuma ayyukan ki.
Allah swt ya ce maka ko miki:
" Karanta littafin nan naka ko naki, yau kai ne, ko ke ce da kanki za ki yiwa kanki hisabi"
Suratu al-isra' - aya ta 14.
As-sa'dy (rh) ya ce:-
Wannan shi ne cikar adalci na Allah swt. Zai bawa bawa littafin sa na ayyukan sa ya ce masa ya karanto da kansa me ya aikata"
Addabariy (rh) ya ce:
" Allah swt zai cewa bawa, karanta ayyukan ka ko ayyukan ki da kanki littafin ne shaidar ki, ba sai an nemi wani mai yin shaida ba.
Qatadah (rh) ya ce:-
Sai ka ko kin karanta littafin nan naka ko naki; koda fa a duniya baki iya karatu ba.
Ibn Katheer (rh) ya ce:
Kowa daga cikin mu sai ya karanta wannan littafin nasa, kuma babu mai tsallake ko harafi guda.
Imamul Qurdubiy (rh) ya ce:-
" Idan da zaka ko zaki boye wani abu ayayin karatun, littafin zai yi magana ya ce ka aikata kaza, ga shi a ciki na an rubuta amma ka boye"
Allah saw ka taimake mu wajen aikata ayyukan alkairi domin a ranar karanta littafin can namu, mu karanta sa cikin farinciki.
-Umar Usman Nakumbo
#Zaurenfisabilillah
TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah
FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/