*MACEN DA BA'A IYA SAKI............*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*FUTOWA TA 👇*
*(15)*
*KADA KI GAZA WAJAN HAQQIN MIJINKI*
Ya "yar uwata mai daraja kada ki gaza wajan gabatar da haqqin mijinki akan haqqinki ki sani mijinki shi ne Aljannar ki kuma shi ne wutar ki.
Wata mata tazo wajan farin jakada babba dan Abdullah Muhammadurrasulullahi saw domin biyan buqatar ta, ya yin da ta gama sai yace da ita kina da miji? Sai tace masa eh sai yace ya ya ki ke masa? Sai tace babu abun da bana yi masa sai abun da na gajiya sai yace ki duba kiga matsayin ki a wajan sa, domin shi ne wutar ki kuma shi ne Aljannar ki.
Ummuna Aisha Allah ya qara mata yarda take cewa da ya ku taran mata da kun san haqqin mazajen ku akan ku da daya daga cikin ku ta share kurar da take dugadugan kafar mijinta da fuskarta.
Haka zalika Asma'u bnt yazid Allah ya qara mata yarda ta zo wajan farin jakada saw tace ya manzan Allah ni wakiliyar mata ce zuwa gare ka, haqiqa ubangijin al'arshi ya turo ka zuwa maza da mata duk kammu munyi imani da kai, amma mu taron mata an tattaremu waje daya, mune masu zama acikin gidajenku, gare mu kuke biyan buqatar ku, mune masu daukar nauyin cikin "ya "ya yenku, ku kuma taron maza an fifita ku akanmu da yin sallar jam'i da juma'a, da duba mara lafiya, da halartar jana'iza, da yin aikin hajji bayan wani hajjin, abun ma da yafi haka shi ne jahadi wajan daukaka Addinin Allah,... Me zamu aikata muyi tarayya daku cikin lada?
Sai manzan Allah saw yace "ki sani biyayyar dayanku ga mijinta da neman yardarsa da binsa cikin abun da yake so hakan yana dai dai da duk wadannan abubuwan da kika lissafa".
Ya "yar uwata mai daraja ki kalli irin girman ladan da mutun yake samu idan ya aikata ko da daya daga cikin wadannan ayyukan amma biyayyar ki ga mai gidan ki yana dai dai da aikata wadannan abubuwan, me kike buqata a nan gidan duniyar da ya wuce neman yardar mahaliccinki.
Don haka ya "yar uwata mai Albarka tun da yanzu kin san daraja girmama mijinki take, babu abun da yake kanki face bin sa da gabatar da haqqinsa akan naki haqqin, muddin kuwa kika lazimci wannan siffar kece wacce nake wa laqabi da macen da ba'a iya saka.
*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*MU HADU A FUTOWA TA 16*
*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
*(Abu Rumaisa)*
🥏08145437040🥏