FA'IDA 05



⚡FA'IDAH⚡ 05

Lokacin da Allah (swt) ya ke bayyana siffofin bayin sa na gari, sai ya ce:-
Su ne masu cewa Ya Allah ka bamu mata da kuma zurriya masu tausayawa, sannan kuma ka sanya mu jagororin masu jin tsoran ka"
Suratu Al-furqan. 

Abdullahi Dan Abbas (r.a.) ya ce:
Abinda ake nufi shi ne: "mutanen kirki, su ne masu rokon Allah (swt) ya basu iyali masu aikata ayyuka na gari, sannan kuma suna nisantar munanan ayyuka"

Ikramah (r.h.) ya ce:-
" Ana nufin su bayin Allah na gari, ba fatan su haifi masu kyawu ba suke, su fatan da suke shi ne; Allah (swt) ya sa su haifi zuriya mai biyayya ga Allah din.

Dhahhak (r.h.) ya ce:
" Ana nufin su bayin Allah na gari, addu'ar su ita ce Allah (swt) ya basu zuriya masu yin biyayya ga Allah din"

Allah (swt) muna rokon ka, 
Ka bawa maza mata na gari, su ma matan ka basu maza na gari, sanna ka sanya zuriyar mu, su zamto masu da'a a gare ka.

Umar Usman Nakumbo

#Zaurenfisabilillah

TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah

FACEBOOK
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)