⚡️ FA'IDAH ⚡️06
HASSADA:
Allah (swt) yana cewa:
"Kawai dai, suna yi ma mutane hassada ne bisa abinda Allah (swt) ya basu daga falalar sa"
...Al-qur'an.
Asali ayar ta sauka ne kan wadanda suke yima Manzon Allah (saw) hassada bisa ni'imar annabta da aka bashi; da kuma sahabban sa bisa ni'imar imani da Allah (swt) ya basu.
Allah sarki, wani daga cikin magabata ya ce:--
"Na rayu cikin mutane masu hassada, to amma da su nake ganewa wani abu na cigaba ya same ni.
Ya ce: Idan naga hassadar ta su ta motsa, to alama ce ta nayi wata nasara"
Duk lokacin da na hadu dai mai ciwon hassada, to maza nake na fara gaishe da shi, ina yin hakan ne, da nufin ko saboda gaishe sa da nayi, hakan ya hana hassadar sa ta motsa.
Imamu Al-Shafi'iy (r.h.)
Khaddab bin Numair ya ce:--
" Shi fa mai hassada, baya da hankali. Ah! to baku ganin da abu mai kyawu da wanda ba shi da kyawu, duka yana iya musu hassada.
To idan ka fahimci mutum ya na da larura ta hassada, menene kuma na damuwa da wanda ba shi da hankali.
Wani daga cikin magabata yana cawa:--
1- Ita hassada ciwo ce; wacce ba'a taba warkewa.
2- Ita hassada juna biyu ce, wacce ba'a taba haihuwar ta.
3- Ita hassada wata abince ce, da bata iya kosar da mai yinta.
Allah (swt) ya kare mu. Ya sanya mana kauna a tsakanin mu da kuma hakuri bisa wata ni'ima da ya bawa wani.
Umar Usman Nakumbo
#Zaurenfisabilillah
TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah
FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/