SADAKA



Da za ka bayar da sadaka da zinaren da girmansa ya kai na dutsen uhud, kyautuwarsa ba za ta kai sahabin annabi (ﷺ) ya yi sadaka da zinaren da bai fi girman rabin mudu ba. 

Su sun kasance suna tsaftace zuciya, suna suturta ayyukansu, hatta wanda za su ba wa sadaka ba su buqatar ya san wanda ya ba shi, don a wajen Allah suke nema. 

Koh sallah idan ba ta wajibi bace, ta fi falala idan ka yi ta a gida musamman inda ba wanda zai gan ka. Mαnzon Allαн(ﷺ) ya kawo masu yin sallah a lokacin da mutane suka yi barci a sahun waďanda za su shiga aljannah da aminci. 

Da yawan mutane za su yi aikin alkhairi tukuru a gidan duniya, amma su je lahira da guzuri dan 'kankani, kasancewar sun ruguza ayyukansu da riya, fāriya da son burge mutane. 

Allah Ya sa mu fi qarfin son zukatanmu.

*✍🏼Ayyub Musa Jebi.*
*ANSAR.*
Posted: 21/09/2020.

*📚 Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*
Post a Comment (0)