GUZURIN RAMADHANA 03
-------------------------
NIYYA
Ita niyya ta kunshi abu biyu ne, ikhlasi da kuma sanin ibadar da za ayin. Kuma muhallinta shine zuciya. Daga sadda ya riski mutum cewa an tabbatar da ganin wata, shikenan sai ya kudurce cewa zai azumci ramadhan *gabaÉ—aya* kuma zaiyi ibadarsa ne don Allah kadai.
Azumin watan ramadhan anayi masa niyyane sau É—aya afarkon azumin, bawai kullum sai anyi masa niyya ba, sai dai idan wani uzuri yasa mutum ya yanke azumin saboda rashin lafiya ko waninsa, to anan idan zai cigaba da azumin to zai sake niyya.
Niyyar kuma ana yintane da dare kafin ketowar alfijir, duk wanda baiyi niyya ba har alfijir ya fito to bashida azumi sai ya rama wannan azumin.
#Zaurenfisabilillah
Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah
Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/