HATTARA DAI ƳAN MATA! 👩🏽‍🦳 .

HATTARA DAI ƳAN MATA! 👩🏽‍🦳



Zan yi amfani da wannan damar ne domin fadakar da ƴan uwana Musulmi musamman (Ƴanmata da Samari) akan wata ɗabi'a da yanzu ta zama ruwan dare a cikin mu.
.
*IDAN KI NA SO NA, KI NUNA MIN;*
.
Wannan zance ne da mafi yawancin samari a yau su ke amfani da shi domin cin ma manufarsu akan budurwa musamman idan suka lura cewa Ta kamu da son su. Su na yin haka ne domin samun damar taɓa jikin budurwa, ko yin kissing ɗinta ko rungumarta da sunan wai nuna Soyayya, wanda yin hakan wani kofa ce da kusantar Zina, wanda kuma Allah Ya yi hani ga kusantar zina.
.
Ya ke Ƴar uwa! Kada ki yarda Gaye ya yi maki wasa da hankali, Ke fa ba ƙaramar yarinya ba ce, Ki yi tunani! Duk namijin da ze neme ki da ki yi Kissing ko Hugging ɗinsa ba tsakani da Allah ya ke son ki ba. Domin saurayi na ƙwarai, shi ne wanda a koda yaushe ya ke da burin kare martabar Masoyiyarsa.
.
Ki sani! Addinin musulunci ya kare maki martabarki, to don me za ki bama wani Ƙazami damar zubar maki da ita.
.
Ka da Ki yarda wani Namiji ya samu damar taɓa jikinki ballantana ya rungumeki ko Kissing ɗinki.
.
Ya kai Ɗan uwa! Ka ji tsoron Allah, Menene ribar ka don ka taɓa jikin macen da ba taka ba, Ka sani,
.
An karbo daga Maƙil bn Yassaar (r.a) ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: *“Da ɗayanku ya taɓa matar da bata halasta a gareshi ba, gara an soka mashi allura ta ƙarfe a kansa”* Ɗabaraani ya ruwaito shi, a al-kabeer 489. Albani ya inganta hadisin.
.
Wannan hadisin na nuna mana cewa Azabar namiji mai taɓa mace, ko macen da ke taɓa Namijin da ba muharraminta ba ya fi a daɓa ma mutum allura a kanshi, saboda haka Wallahi mu ji tsoron Allah domin yana kallonmu a duk inda muke.
.
Kuma haramunne yin hannu tsakanin Namiji da Mace matuƙar ba Muharraman juna bane, hadisi ya tabbata daga Annabi (ﷺ) cewa ya ce: *“Ni ba na yin hannu da mata....”* har zuwa ƙarshen hadisin, Kuma Allah (ﷻ) Ya ce: “Haƙiƙa abin koyi kyakkyawa ya kasance a gareku wajen manzon Allah” Don haka dole ne a kan mu kada mu yi hannu da mata, domin koyi da Annabi (ﷺ).
.
Ya Ƴan uwana Musulmi, Ni ina yi maku nasiha akan ku Nisanci duk wani abu da ze kai ku ga fushin Ubangiji.
.
Ya ke Ƴar uwata mai daraja ka da ki yarda ku keɓance da saurayi ko wani namiji ba tare da wani muharramin ki a wajenba, domin Annabi (ﷺ) ya ce: *“Wanda ya kasance yana Imani da Allah da Ranar lahira, to kada ya kuskura ya kaɗaita da mace ba tare da muharraminta na tare da ita ba, domin na ukunsu shi ne Shaiɗan”*
.
Daga ƙarshe, Ya ku Ƴan uwana Muminai Maza da Mata! Ina tunatar da ku Wasiyyar Allah a gareku a inda yake cewa:
.
*“Ka ce da muminai maza su kame ganinsu, kuma su kiyaye farjinsu. Wannan shi ya fi tsarki a gare su. Haƙiƙa Allah Masanin abin da su ke aikatawa ne. Ka ce da muminai mata su kame ganinsu, kuma su kiyaye farjinsu. Kada kuma su fito da adonsu, saidai abinda ya bayyana daga gare shi, kuma su yi lulluɓi da mayafansu a kan wuyan rigunansu. Kuma kada su bayyana adonsu sai ga mazajensu, ko ƴaƴayensu, ko ƴaƴayen mazajensu, ko ƴan uwansu maza, ko ƴaƴan ƴan uwansu maza, ko ƴaƴan ƴan uwansu mata, ko mata (musulmai) ƴan uwansu, ko kuma abinda hannayensu suka mallaka (bayi), ko kuma mabiya ba masu bukatar mata ba daga maza, ko kuma ƙananan yara waɗanda basu san sha'awar al'aurar mata ba. Ka da kuma su buga ƙafafunsu don a gane abin da suka ɓoye na adon ƙafafunsu (wato mundaye). Kuma ku tuba ga Allah gaba ɗayanku ya ku waɗannan muminai don ku rabauta”*. (An-Nur: 30, 31)
.
Anan ne zan dakata da rubutu Na, Allah Ya shiryar damu a hanya madaidaiciya.
.
*Ayyub Musa Jebi.*
*08166650256.*
*26/01/2018.*

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
Post a Comment (0)