KU KEƁANCE LOKUTA NA MUSAMMAN DOMIN ZAMA DA ZANTAWA DA IYALANKU

KU KEƁANCE LOKUTA NA MUSAMMAN DOMIN ZAMA DA ZANTAWA DA IYALANKU πŸƒ


πŸƒ Ka keΙ“ance wani lokaci na musamman ga iyalinka, kuyi hira, kuyi raha, kuyi wasa, kaji damuwoyinsu, ku tattauna al'amuran gida, rayuwanku anan gaba, cigabanku duniya da lahira, matsalolinku na gida don samun maslaha, tarbiyya da karatun Ζ΄aΖ΄anku.... da sauransu.

πŸƒ Manzon Allah (SAW) ya kasance yana baiwa iyalansa kulawa, zama dasu, fira dasu, jin damuwoyinsu da nusar dasu ababen da zasu amfanesu duniya da lahira. har yace: *"Wanda yafi kowa kyautatawa a cikinku shine wanda yafi kowa kyautatawa iyalinsa, Ni ko nafi ku kyautatawa iyalina".*

πŸƒ Hira dasu baya kawo raini ko wargi hasalima shike Ζ™ara shaΖ™uwa, Ζ™auna, mutuntawa da girmamawa. Manzon Allah (SAW) yana hira da iyalansa, suyi wasa suyi raha, kuma hakan bai sa ya rasa girma a idonsu ba!

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:πŸ‘‡
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)