HUKUNCIN KUSANTAR MACE MAI SHAYARWA

HUKUNCIN KUSANTAR MACE MAI SHAYARWA 



:

TAMBAYA❓
:
Assalamu alaikum da fatan Malam yana nan lafiya. Wata tambaya nake dauke da ita kamar haka.

Ni Mace ce mai saurin daukar ciki, wani lokacin ma nakan samu cikin wani yaron tun kafin in yaye wanda nake Shayarwa. kuma idan na samu cikin nan ina da yawan laulayi.

Wahalar da nake sha tasa na hana Maigida ya kusanceni, don gudun kar in sake daukar juna biyu da wuri, domin wanda nake shayarwa yanzu haka bai fi shekara guda da rabi ba.

Shin ya halatta inci gaba da nesantar Maigidana har sai na yaye yarona, saboda tsoron cutuwar da nakeyi? Ko kuwa akwai laifi, tunda hakkinsa ne?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus Salam.

Shi dai Jima'i hakki ne wanda Ma'aurata suke dashi akan Junansu amma Miji ne yake da iko dashi. Kuma babu wani lokaci wanda aka haramta wa Miji ya kusanci Matarsa sai dai lokacin da take cikin Jinin Haila, ko jinin haihuwa.

Dangane da kusantar Mace mai shayarwa kuwa, akwai hadisin da Imamu Muslim ya ruwaito daga Sayyidah Judaamatu bintu Wahab Al-Asadiyyah (ra) tace taji Manzon Allah (saww) yana cewa:

"NAYI NUFIN IN HANA SADUWA DA MACE MAI SHAYARWA, AMMA SAI NAGA CEWA MUTANEN RUM DA FARISA SUNA YI, AMMA HAKAN BAI CUTAR DA 'YA'YANSU BA"
(Sahihu Muslim, hadisi na 1442).

Don haka babu laifi don mijinki ya sadu dake yayin da kike shayarwa. Domin kuwa hakkinsa ne, bai kamata ki hanashi ba.
Wannan hanashin da kikeyi zai iya jefashi cikin tunanin wata hanyar da zai bi domin samun biyan bukatarsa. Watakila ya fara tunanin Qara miki abokiyar zama, Wani ma in ba mai tsoron Allah bane, sai ki jefashi cikin Zina.

Manzon Allah (saww) yace: "DUK MATAR DA MIJINTA YA KIRATA ZUWA SHIMFIDARSA, AMMA BATA JE MASA BA, HAR YA KWANA YANA FUSHI DA ITA, MALA'IKU SUNA TSINE MATA HAR SAI TA WAYI GARI"

Kiji tsoron Allah kar ki zama daga cikin wadannan matan wadanda Mala'iku suke tsine musu.
Kuma tunda kince Yaron da kike shayarwa yakai shekara guda da rabi, ai ba zai cutu ba koda kin samu juna biyu. Domin kuwa akan yaye yaro wani lokacin tun daga Watanni 18.

Dangane da larurar laulayin ciki kuma, ya kamata kuje wajen likitan haihuwa domin samun shawarwari.

Idan har laulayin zai cutar da Yaron da kika shayarwa sosai, ko arasa ransa, to Malamai sunce zaku iya yin Azalo, ko kuma kuyi allurar da zata tsayar da daukar cikin zuwa wasu watanni. Mutukar dai ba zai cutar dake ba.

Wallahu a'alam.

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaÉ—a wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH


Post a Comment (0)