HUKUNCIN MACE DA JININ HAILA YA ZO MATA TANA CIKIN

HUKUNCIN MACE DA JININ HAILA YA ZO MATA TANA CIKIN JANABA
:
TAMBAYA❓
:
mace ce mijinta yasadu da'ita amma kafin tayi wanka sai haila tazo mata, shin wanka biyu zatayi kenan ko yaya?
:
AMSA👇
:
Alal-haƙiƙa ansamu saɓānin mālamai dangane da hukuncin matar da tasadu da mijinta kokuma tayi mafarki amma kafin tayi wankan-janaba sai jinin-haila yazo mata, kokuma yakasance mace tana cikin jinin-hailarne kuma sai tayi mafirki har maniyyi yafito mata,
:
mazhabin hanābila dakuma wasu daga cikin mālamai suntafi akan cewa ba wajibi bane akanta sai tayi wankan-janaba, danhaka zata jirane harsai jinin-hailar yaɗauke sannan tayi wanka, amma inda zatayi wankan-janabar alokacin datake jinin-hailar, shikenan wankanta yayi kuma hukuncin janaba yasauka daga kanta, shikuma jinin-hailar hukuncinsa yana tare da'ita harsai idan ya yanke sai tayi masa wanka, amma idan batayi wankan-janabarba harsaida jinin-hailar yaɗauke mata, mafi yawan mālamai waɗanda suka haɗa harda mazhabobin nan guda huɗu sanannu, suntafine akan cewa idan tazo wankan zata ƙulla niyyar wankan-janaba da wankan-haila azuciyarta saitayi wanka guda ɗaya ya wadatar, amma wasu daga cikin mālamai suntafine akan cewa dolene sai tayi wanka biyu kowanne nasa dabam, saidai maganar farko da'akace zatayi wanka ɗayane da niyya biyu tafi inganci,
:
amma mazhabin mālikiyya dakuma hanābila sukace idan da zata ƙulla niyyar wankan-janaba kaɗai azuciyarta ko wankan-haila kaɗai, to iya abinda ta ƙulla niyyar akansane kawai yagushe daga gareta banda ɗayan, domin mαиzoи aʟʟαн(ﷺ) yace:
:
"إنما الأعمال بالنيات، وإنما لكل امرئ ما نوى"
ma'ana:
lallai ayyuka (na ibada) saida niyya, kuma kowanne mutum (ana karɓar aikin) da yayiwa niyya ne,
:
saidai mazhabin shāfi'iyya da hanafiyya sukace koda niyyar wanka guda ɗaya kaɗai ta ƙulla azuciyarta sukace yayi saboda zai iya ɗauke hukuncin ɗaya wankan, to amma maganar mālikiyya da hanābila tafi inganci dakuma dalili mai ƙarfi,
:
danhaka magana mafi inganci wacce mafi yawan mālamai suka tafi akanta shine, idan jinin-haila yazowa mai janaba kokuma janaba tazowa mai haila, to zata dakatane harzuwa lokacin da jinin-hailar zai ɗauke mata, sai ta ƙulla niyyar wankan-janaba da wankan-haila azuciyarta sai tayi wanka guda ɗaya ya isar mata,
:         
           ✍🏼mυѕтαρнα uѕмαи
            
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
:
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH



Post a Comment (0)