HUKUNCIN KYAUTAR LADAN IBADA GA ANNABI S.A.W?
*TAMBAYA*❓
:
Assslam alaika warahamatullah wabrakatuhu malam ina maka fatan alkairi tambaya ta itace wani bawan Allah ne idan yayi sallah nafiloli sai yace Allah ya bawa Annabi ladan menene hukuncin hakan ya halatta?
:
*AMSA*👇
:
To dan uwa wannan bidi'a ne ba addini bane kuma ya aikata abinda magabata basu yiba ya kamata mutum musulmi yasan abinda yake ya dinga aikata abinda shari'a tace yayi, wannan karancin tunani ne rashin sanin ya kamata ne ai kai baka isa kabawa Annabi S.A.W lada ba duk duniya babu wanda yakai Annabi tarin lada mai yawa kana tsammanin ladanka zai kara masa wani abu babu abinda zai kara masa domin Allah ya yafe masa idanma yayi kuskure don haka wannan bidi'ane ba addini bane kuskure ne a kiyaye abinda babu asali a musulunci.
Sannan ba'a daukan lada a bawa wani bazaka iya daukan lada kace na bawa wane ba kamar kayiwa iyayenka sallah ko karatun Alkur'ani kace a basu ladan sai dai kayi wani abu na sadakatul jariyya wadda zata riskesu
Allah shine mafi sani
Amsawa:- Dr. Abdallah Gadon kaya
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ