YAWAITA NEMAN GAFARAR ALLAH (ISTIGHFAARI):
Allah Ta’ala Ya ce: “Kuma Allah bai kasance Yana yi musu azaba ba alhali kuwa Kai kana cikin su, kuma Allah bai kasance Mai yi musu azaba ba alhali kuwa su na yin istighfaari” Suratu al-Anfaal 33.
Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Allah Ta’ala Ya yi masa rahama a ƙarƙashin fassarar wannan aya ya ce:
“Rayuwar Annabi a cikin mutane aminci ne daga azaba, haka kuma yin istighfaari aminci ne. Wanda ke son wadata da aminci daga Allah, sai ya lizimci istighfaari da bin sunnar Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce:
“Duk wanda yake so takardun ayyukansa su faranta masa rai ranar al-Ƙiyama, to ya yawaita istighfaari”. Albaihaƙiy ya fitar da hadisin daga al-Zubair bn al-Awwaam 1/440,441.
*SHUGABAN DUKKAN ISTIGHFAARI*
Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce: Shugaban dukkan istighfaari, shi ne mutum ya ce:
*ALLAHUMMA ANTA RABBIY LAA ILAAHA ILLAA ANTA, KHALAƘTANIY WA ANA ‘ABDUKA WA ANA ‘ALA ‘AHDIKA WA WA’DIKA MASTAƊA’TU A’UDHU BIKA MIN SHARRI MAA SANA’TU ABUU’U LAKA BI NI’MATIKA ‘ALAIYYA WA ABUU’U BI ZANBIY, FAGHFIRLIY FA’INNAHUU LAA YAGHFIRUZ ZUNUUBA ILLAA ANTA”*
Duk wanda ya karanta wannan a cikin yini yana mai sakankancewa da abun da ya faɗa sai ya mutu a wannan yini kafin yamma, to yana cikin ‘yan Aljanna. Haka nan duk wanda ya karanta da yamma yana mai sakankancewa da ita sai mutuwa ta riske shi kafin ya wayi gari, to yana daga cikin ‘yan Aljanna. Buhari ya fitar da hadisin 6306 hadisin Shaddaad bn Aus, Radhiyallahu anhu.
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Dan uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria