IRIN WANNAN RAYUWA

Murɗewar ciki sakamakon tsananin yunwa ne yayi sanadiyar farkawar sa daga barci cikin tsulutsainin dare. Hakan ya sa ya kurɓi ruwa sannan ya ɗaura alola, nan take ya tsaida nafila, har lokacin sallar asuba yayi. Kimanin kwanaki huɗu kenan bai ci isasshen abinci ba.

Bayan dawowar sa daga sallah, iyalinsa ta tabbatar masa da tsananin yunwar da take ji, da kuma rakin da yara suke ta yi cikin dare.

Bai samu zama ba, ya fito fafutuƙar nema. Bayan awa biyu, ya dawo da abincin da bazai wadatar da shi ba, ballantana ya wadatar da ahalin sa.

Suna cikin tsakura, bayan sun ware wa yara na su, sai ga yaran sun dawo daga makaranta. Da suka nemi ba'asi, sai yaran suka tabbatar musu da an kore su kuÉ—in makaranta ne.

Ba su kammala jinjina wannan jarabta ba, sai ga mai gidan hayar da suke ciki ya banko kai cikin gidan. Yana shaida masa cewa, matsawar nan da awa 3 bai kawo kuÉ—in haya ba, zai kore shi daga gidan.

Fitar sa ke da wuya, ya nufi manajan kamfanin da yake aiki, da bukatar ya ara masa kuÉ—in da zai biya hayar gidan sa. Amma manaja ya hana shi.

Ya koma wurin hamshakin attajirin unguwar su, don ya taimaka masa. Amma ya ki.

Ya kira ƴan uwan sa na jini don su taimaka masa, amma babu wanda ya ɗaga kai. Nan hankalin sa ya daɗa harzuƙa.

Yayi posting a facebook don abokan sa na facebook su taimaka masa, amma me zai samu, bai wuce likes 2, da comment 3 ba, su ma comment in na fatan alheri ne.

Yana dawowa, ya tarar da iyalan sa a waje. Mai gidan hayar nan ya watsar masa da kayayyakin sa da ahalin sa waje, sannan ya kulle gidan. Ga shi kuma dare yayi. Nan hankalin sa ya ƙara dunguzuma.

Ya ɗauko wayar sa, ya tura sakonni ga abokan sa, kusan mutane 210. Amma mutane 10 ne kacal daga cikin su, suka mayar da sakon. 6 daga cikin su ƙorafi suke akan rashin kuɗin da suke ciki. Ɗaya daga cikin huɗun ne ya turo dubu 20. Sauran huɗun duk fatan alheri da jajanta masa suke yi. Duk sauran sun ki ɗaukar wayar sa.

A ƙoƙarin sa na tsallaka hanya ne, Tankar mai ta buge shi, nan take ruhin sa ya rabo da gangan jikin sa.

Kan ka ce wani abu, labarin Mutuwar sa ya karaÉ—e ko ina.

Abokan sa na Facebook sama 2250 ne suka tura sakon ta'azziya, jajantawa da fatan aljannah a timeline in sa.

Hamshakin mai kuÉ—in unguwar su, ya aiko da naira dubu 100, da shinkafa buhu 1, da cefane ga iyalan sa, don su yi zaman makoki.

Mai gidan hayar da ya kore su, nan take ya zo ya buɗe, ya musu izini su shiga, dan su yi masa sutura, kuma su karɓa ta'azziya.

Abokan sa, suka yi karo-karon kuÉ—i, suka haÉ—a sama da Naira dubu 300, suka kawowa iyalan sa, don rage zafin zaman makoki.

Abokan aikin sa, suma sun haÉ—a kuÉ—in da ya kai dubu 100 suka kawowa iyalan sa.

IRIN WANNAN RAYUWAR NE MUKE CIKI YANZU.

BA A DARAJA RAYAYYE, SAI DAI MATACCE.
BA A TAIMAKON KA DON KA AMFANA, HAR SAI AN TABBATAR BAZA KA AMFANA BA.

HAKA NE KOYARWAR ADDININ MU?.

INA ÆŠAN ADAMTAKA ANAN?

© Prof. Sufyan

Post a Comment (0)