💫Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi.
*✨سؤال وجواب في أحكام الصيام.*
Wallafar:
*Sheikh Muhammad bn Salih Al-Uthaimin.*
.
.
(6) ABUBUWAN DA BA SU KARYA AZUMI.
*2. Haɗiye Miyau, Majina da Kāki (sputum):*
Tambaya I: Shin haɗiye miyau yana ɓata azumi?
Amsa: Haɗiye miyau ba ya ɓata azumi.
.
Tambaya II: Menene hukuncin haɗiye majina ko kāki?
Amsa: Idan be kawo baki ba, azumi yana nan. Idan kuwa sai da ya zo baki sannan ya haɗiye shi, akwai zance biyu na malamai, wasu malaman suna ganin cewa azumin yana nan wasu kuma suna ganin azumin ya ɓaci. Idan irin wannan abu ya faru, sai mu koma ga asalin tushen matsalar (a duba hujja daga Alqur'ani da Sunnah). Asali shi ne majina ko kāki ba ya ɓata azumi, kuma tunda babu wata hujja da ta yi inkarin hakan, za mu tafi a kan cewa haɗiye shi ba ya karya azumi.
Mu haɗu a tambaya ta gaba.
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*▫️Ansar.*
*📚Irshadul Ummah.*
Ku kasance da mu a Whatsapp ta wannan number *08166650256.*
Telegram:
https://t.me/irshadulummah1