LOKACIN HANA BARCI
Tambaya
Allah karawa Malam lafiya da nisan kwana.
Me ingancin maganar da ake cewa ba kyeu kwanciya lokacin mangrib?
Amsa:---
Babu laifi a yi barci da yamma: a bayan la'asar zuwa Magrib. Hadisi mai hana yin hakan ba shi da asali. [SILSILATUD DHA-I'FA; 39]
A bayan Sallar Magrib ne kađai a ka hana yin barci, kowane Hadisi mai hanawa a wani lokaci daban, bai inganta ba. [FATA'WAL LAJNA; 26/147]
Bai kamata a yi barcin safe kafin rana ta bullo ba, da kuma kafin buya ba, don lokutan zikiri ne, amma babu laifi idan anyi.
[SAHI'HUL ADAB; 1242]
Amsawa :-- Sheikh Abdurrazak Yahaya Haifan
17-11-2021
Zaku Iya bibbiyar mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248