MIJINA YA SAKE NI SAI YA MAIDANI, NI KUMA BANA SON NA KOMA GIDANSA.



MIJINA YA SAKE NI SAI YA MAIDANI, NI KUMA BANA SON NA KOMA GIDANSA.
:
*TAMBAYA*❓
:
Idan mijina ya sakeni saki 1 da cikin wata 6 a jikina, sai daga baya kafin na haihu sai yace ya dawo dani, ni Kuma naki komawa tunda Daman hakuri nakeyi dashi yazo ya sakeni batare da nace yasakeni ba, Kuma mlm har cikin Raina banason sake komawa gidansa sabida gaba daya yafita a Rai na, Babu sonsa azuciyana, meye matsayina donshi yanacewa ni matarsace nikuma inacewa ba matarsa bace don yana ikirarin zaiga ubanda zai dauramin aure, ataimakamin da amsa, bissalam🙏🙏
:
*AMSA*👇
:
 Ya Fi ki Gaskiya Anan.
 Duk Mutumin da ya saki matarsa. Matukar dai Iddarsa bata Cika Akanta ba. Sai kuma Yace ya Maidata. To ba Makawa ta Maidu. Ko tana so ko bata so. Sabida Faɗin Allah da Yake Cewa "MAZAJENS SU SUNE SUKE DA HAKKIN MAYAR DA SU AKAN HAKAN IDAN SUNA NUFIN MASLAHA".
 Yadda ake Yiwa Irin Wadannan Mazajen Wadanda Basa Son Zaman Lafiya. Domin Suna Maida Mace ne dan Su Azabtar da Ita. Ba don Sucigaba da zama don Maslaha ba, Sabida Sun San Allah ya basu wannan Damar.
 Idan har Akwai Cutarwa da Wulakanci da Sauransu. Wanda Wannan Halayen Nasa ne ma yasa Kika ji ya Fita a Ranki. Har ta kai da son sa baya Zuciyarki. Kuma baki da Ra'ayin Komawa Gidansa. Da Zarar ya Sake ki. Sai Ki Hada kayanki ki Bar Garin da yake, Ki Kashe Wayarki, ko ki cire Layin da ya san ki da shi, ki Lalata Whatsapp Naki, ya dena Ganinki Online. Ki tafi Wani Gari Chan gurin Wasu yan Uwanki, inda ba zai sami Labarin halin da kike ciki ba. Inda ba Zai sami damar Ganinki ba, inda ba zai sami damar yin Magana da ke ba. Ko ta Hanyar Sako. Bare ma Yace ya Maidaki.
Kinga kenan a Haka zai gaji da Neman Labarin ki, ba zai Samu ba. Idan iddarsa ta cika a Kanki. Sai ki dawo. Idan kin dawo kuma ya Ganki ko Yace ya Maidaki, Shirme ya ke yi, Sabida Iddarsa ta Cika Akanki. Anan ne kuma Bashi da Ikon Maida ki. Sai dai ya shiga Sahun Manema. Idan Allah yayi da shi za'a yi. Ma'ana Bayan Ya Gyara Halayensa, yayi Alkawarin ba zai sake ba. Kuma Allah ya Rubuta Zamanki da shi Bai Kare ba. Sai ku Koma. Idan kuma Allah yayi da wani za'a yi ba shi ba. Shikenan Shima sai ya Nemi Wata.

Allah Shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 081377873797

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)