SAHABI JIKAN SAHABI, BABAN SAHABI
*TAMBAYA*❓
:
Aslm, don Allah akwai sahabin da kakansa sahabi ne, babansa sahabi, dansa kuma sahabi?, ina son karin bayani malam?
:
*AMSA*👇
:
To malam sahabin da yake kakansa sahabi, dansa sahabi, babansa sahabi, shi ne: Abdurrahman dan Abi-bakr bn Abi Khuhafah kamar yadda Ibnu Salah da Ibnul-jauzy suka ambata. Saboda mahaifinsa Abubakar sahabi ne, hakanan kakansa Abu khuhafah shi ma sahabi ne sannan dansa Muhammad sahabi ne, Ibnu Hajar yana cewa: Ba mu san mutum huɗu da 'ya'yansu wadanda suka ga Annabi S.A.W ba sai wadannan.
Abin da yake nufi shi ne: Muhammad da mahaifinsa Abdurrahman da kakansa Abubakar da kakansa na biyu Abu-kuhafah dukkansu sun ga Annabi S.A.W, don haka su kaɗai suka samu wannan darajar, Allah ya kara musu yarda.
Don neman karin bayani duba tarjamar Muhammad a Usudul-gabah a lamba ta: 6083.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ