SHIN YA HALATTA MUTUM YAYI RAKA'ATANUL FAJR IDAN BAI SAMI JAM'IN ASUBA BA?
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum
YA HALATTA MUTUM YAYI RAK'ATAYIL FAJR IDAN BAI SAMU JAM'IN SALLAR ASUBAH BA HAR GARI YAFARA HASKE, ZAI FARA YIN SALLAR ASUBAH NE KO KUMA NAFILAR ZAI FARA YI?
JAZAKALLAH KHAIR
:
*AMSA*👇
:
ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ .
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ،
Ya hallata mutum ya fara yin rak'atayil fajr sannan yayi sallar asuba idan ya rasa jam'i asuba.
Da farko dai wajibi ne akan kowanne musulmi ya kiyaye sallah akan lokacin ta. Allah madaukakin sarki yace:
_ﺇﻥ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻛﺎﻧﺖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻛﺘﺎﺑﺎً ﻣﻮﻗﻮﺗﺎ._
_Lalle ne sallah ta kasance akan muminai farilla mai kayyadaddun lokuta._
Lokacin sallar asuba shine daga fitowar alfijir na biyu har izuwa hudowar rana.
Baya halasta jinkirta sallah har lokacin ta ya fita. Saboda yin haka da gangan yana daga cikin manyan kaba'ira. Sabanin wanda ya manta sallar ko kuma barci ya rinjaye shi ba da gangan ba, shi wannan abun yiwa uzuri ne.
*Manzon Allah ﷺ* yace:
_"ﻣﻦ ﻧﺴﻲ ﺻﻼﺓ ﺃﻭ ﻧﺎﻡ ﻋﻨﻬﺎ ﻓﻠﻴﺼﻞ ﺇﺫﺍ ﺫﻛﺮﻫﺎ، ﻻ ﻛﻔﺎﺭﺓ ﻟﻬﺎ ﺇﻻ ﺫﻟﻚ"_
_*ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.*_
*Fassara:*
_Wanda ya manta sallah ko yayi barci akanta (barci a lokacinta) to ya sallaceta idan ya tina ta (sallar), kuma babu kaffara sai wannan (ramawar)._
_*Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.*_
Sallar asuba raka'a biyu ne, a gabanin su akwai raka'a biyu na nafilah ana kiransu *"Sunnatul Fajr"* ko *"Sunnatus Subhi"* ko *"Ragiibatul Fajr"* ko *"Rak'atayil Fajr".*
Idan mutum ya rasa jam'in asuba ya halatta mutum yayi rak'atayil fajr kafin yayi sallar asuba. Koda rana ta fito ne zai iya yin sallar rak'atayil fajr kafin yayi sallar asuba. Amma fa ba wanda ya rasa jam'i da gangan ba, saidai kamar wanda barci ya rinjayeshi har gari ya waye.
Kamar yadda yazo a Bukhari da Muslim da Sunan Abu Dawuda cewa:
_Haqiqa ya tabbata cewa barci ya rinjayi *Manzon Allah* da Sahabbansa a wata tafiya, basu farka ba har rana tafito sai suka sallaci rak'atayil fajr sannan suka sallaci asuba._
A wata ruwaya akace
_*Manzon Allah ﷺ* ya umarci da a kira sallah sannan ya sallaci raatiibat (rak'atayil fajr), sannan ya umarci ayi iqaamah bayan haka sai ya sallaci farillah (sallar asuba)._
Saboda haka ya halatta a fara yin rak'atayil fajr kafin sallar asuba idan an rasa jam'in asuba koda rana ta fito ne.
والله أعلم،
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ