ZAN IYA HULDA DA MAI KUƊIN LUKUDI ?
*TAMBAYA*❓
:
Assalama alaikum. Malam dan Allah Ina aiki ne akarkashin wani Alhaji Amman a nazargin sa da wai kuɗinsa bana halal bane wasu suce ɗan luwadi ne wasu kuma suce kuɗin lukudu ne, ina so in san ya dace na cigaba da mai aiki ko inbari Allah ya kara lpy da ilimi da kaifin basira ameen
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikum assalam, Ya wajaba ka tabbatar da hakan kafin ka yanke hukunci.
Ba'a gina hukunci a musulunci akan shakka ko zato mara rinjaye, saboda wani sashen zaton zunubi ne kamar yadda aya ta (12) a cikin suratul Hujraat ta tabbatar da hakan.
Idan wani bangare na kasuwacinsa halal ne wani kuma Haram ne za ka iya hulda da shi, saboda Annabi S.A.W ya yi mu'amala da yahudawa kuma a cikin dukiyarsu akwai halal akwai kuma haram.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ