SHIN WANNAN AURAN YA DAURU ?

SHIN WANNAN AURAN YA DAURU ?


السلام عليكم ورحمة الله وبركاته.
احسن الله إليكم وزادكم الله التقوى.
Tambayarmu ita ce: saurayi ne ya cewa buduruwarsa wai yaushe za mu yi aure ne?
Sai buduruwar ta ce ko gobe ne idan ka shiriya za mu yi, sai yace sadaki fa sai buduruwar tace ka yi sadaka da shi, sai ya je ya tara shedu 4 sai yayi sadaka da kudin sadakin.

*Amsa*
Wa alaikum assalam wa Rahmatullah

Bai dauru ba tun da babu waliyyi a auran, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Yana cewa : "Duk matar da ta Yi aure ba tare da iznin waliyinta ba, to auranta batacce ne"

Allah ne mafi Sani.

*Dr Jamilu Yusuf Zarewa*
23/02/2022


Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a kasance damu a 

FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM⇨
https://t.me/Miftahulilm2

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)