YA ZAFI?

'Yan uwa ya muke fama da wannan yanayin na zafi? ☺ 


Haqiqa na san wasu suna matuqar takura a irin wannan yanayin musamman a ire-iren gidajenmu na Yā ku bāyi inda babu wadatar wutar lantarki ballantana na'ura mai ba da iska (fan or AC). Duk da kasancewar windows da Doors da muke da su a ďakunanmu, hakan bai hana mu korafi a kan wannan yanayi ba domin iskar da ke shigowa ta waďannan kafofi ba ta gusar da zafin da yake surarowa yana ratsa gangar jikin mu, hakan ke wajabta mana taqaita suturar jikinmu, da yawaita watsa ruwa wa jikinmu, wasun mu ma a waje suke kwana don dai a samu sauqi. 

Ya kai ďan uwa! So nawa ka ta6a hasashen yadda zamanka a Qabarinka zai kasance tunda shi rami ne da babu qofar shige da fice na iska, babu wajen fita shan iska sannan babu ruwan watsa wa a jika. Ka duba yadda qasa take ďaukan zafi yayin da rana mai zafi ta dake ta, ya kake tunani idan kana a qarqashin qasa a wannan hali. Anya mai yin irin wannan tunanin zai yi gangancin biye wa rayuwar duniya kuwa har ya manta da dokokin Mahaliccinsa?!

Domin tsira daga dawwamammen zafi da samun ni'ima mai ďorewa a rayuwarka ta Qabari, Yi abin da Allah da ManzonSa suka umarta, Kyale abin da Allah da ManzonSa suka hana. Haqiqa za ka yi kwanciya a Qabari irin kwanciyar ango a darensa na farko. 

*أللهم إنا نعوذ بك من عذاب القبر 👏🏿*

*✍🏽Ayyub Musa Giwa.*
*▫️Ansar.*

*📚Irshadul Ummah.*
Post a Comment (0)