Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi

*💫Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi.*


*✨سؤال وجوب في أحكام الصيام.*

Wallafar:
*Sheikh Muhammad bn Salih Al-Uthaimin.*
.
.
*(3) ABUBUWAN DA SUKE KARYA (ƁATA) AZUMI.*

*Tambaya:* Wasu abubuwa ne suke karya azumi?

*Amsa:* Abubuwan da suke karya azumi kamar yadda Allah Ya lissafa cikin Alqur'ani mai girma su ne: Cin abinci, shan abin sha, jima'i, da duk wani abu da yake da alaƙa da ci da sha mai amfani ko mai cuturwa, kaɗan ko dayawa. Don haka, zuƙar hayaƙi (smoking) yana karya azumi.

Na ukun: *Jima'i,* wannan shi ne mafi tsananin abin da ke karya azumi saboda yana wajabta yin kaffara; 'Yanta bawa, idan hakan ba zai yiyu ba, sai ka azumci watanni biyu a jere, idan ba za ka iya ba, sai ka ciyar da miskinai sittin (60).

Na hudu: Fitar maniyyi ta hanyar jin daɗi, wannan ba ya wajabta kaffara. Kaffara tana wajaba ne kaɗai ta hanyar jima'i.

Na biyar: Allurar abinci ko abin sha (nutritious injection), amma allurar da ba ta abinci ba, ba ta karya azumi (ko da ta jijiya ne ko wadda ake yi a tsoka).

Na shida: Ƙaƙalo amai da gan-gan.

Na bakwai: Jinin haila ko na biƙi (jinin haihuwa); Idan wannan jinin ya fita azumi ya karye ko da kuwa saura dakika ɗaya (a second) rana ta faɗi, amma idan ya fita bayan faduwar rana koda da dakika ɗaya ne, azumin ya yi.

Na takwas: Fitar jini ta hanyar yin ƙaho, Annabi (ﷺ) ya ce: *«Wanda ya yi ƙaho da wanda aka yi mawa sun karya azuminsu».* [Ahmad da Albani, Al-Irwa: 931). Wanda ya fitar da jininsa ta hanyar ƙaho azuminsa ya lalace, idan mai yin ƙahon ya yi koyi da yadda ake yi a zamanin Annabi (ﷺ) (zuƙo jinin ta ƙaho), shi ma azuminsa ya lalace, amma idan ya yi ne ta hanyar da ba sai an zuƙi ƙahon ba, azumin mai ƙahon ya yi amma na wanda aka yi wa ƙahon ya lalace.

*Abin lura:* Idan waɗannan abubuwan masu karya azumi suka faru a kan musulmi baligi a yinin Ramadana, waɗannan abubuwan sun hau kanshi:

_(i) Ya aikata zunubi._
_(ii) Azuminsa be inganta ba._
_(iii) Zai kame bakinsa daga ci da sha har zuwa lokacin buɗa baki._
_(iv) Dole ne ya rama azumin._

Wanda ya karya azuminsa ta hanyar jima'i, abu na biyar ya faɗa kanshi bayan huɗun da aka lissafa a sama, shi ne _dole ne ya yi kaffara._

Mu sani cewa, waɗannan abubuwa masu karya azumi suna lalata azumi ne a bisa waɗannan sharuɗɗa masu zuwa:

_(i) Idan ya kasance yana da ilimi a game da su._
_(ii) Yana sane (ba mancewa ya yi ba)._
_(iii) Ya yi ne da gan-gan._

💠 Wanda ya ci abinci cikin rashin sani, azuminsa ya yi. Kodai be san lokaci ba, ko kuma be san hukuncin ba. Misali, ya tashi ya yi sahur cikin rashin sanin cewa alfijir ya keto, azuminsa ya yi saboda ya jahilci lokacin. Ko wanda ya yi ƙaho be san cewa yin ƙaho yana lalata azumi ba, shi ma azuminsa na nan saboda be san hukuncin ba.

💠 Idan mutum ya ci abinci cikin mantuwa, azumisa yana nan.

💠 Idan aka tilasta mutum ya aikata wani abin da yake karya azumi ba tare da son ranshi ba, azuminsa yana nan.


Mu haɗu a tambaya ta gaba.
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*▫️Ansar.*

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*

Telegram:
https://t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)