Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi 07

*💫Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi.*


*✨سؤال وجواب في أحكام الصيام.*

Wallafar:
*Sheikh Muhammad bn Salih Al-Uthaimin.*
.
.
(6) ABUBUWAN DA BA SU KARYA AZUMI.

*1. Asuwaki, makilin (tooth paste), kwalli, maganin ciwon ido (eye-drop) da turare:*

Tambaya I: Menene hukuncin yin asuwaki bayan hudowar rana a yinin Ramadana?

Amsa: Yin asuwaki a Ramadan gabanin ko bayan hudowar rana sunnah ne, kamar yadda yake a sauran watannin domin hadisan Annabi (ﷺ) ba su keɓance cin asuwaki da wani lokaci ko yanayi ba.
.

Tambaya II: Menene hukuncin goge baki da makilin (tooth paste) a yinin Ramadana?

Amsa: Babu wani laifi a cikin goge baki da makilin sai dai in ya shiga ciki. Abin da ya fi shi ne kada a yi amfani da shi saboda akwai yiyuwar zai iya shiga ciki ba tare da an sani ba.
.

Tambaya III: Menene matsayin wani ya yi amfani da kwalli, eye drop, ear drop ko nose-drop a Ramadan?

Amsa: Babu laifi don an yi amfani da kwalli ko eye drop koda kuwa an ji ɗanɗanonshi a maƙogoro, ba zai ɓata azumi ba.
.

Tambaya IIII: Shin shāƙar ƙamshin turare kamar Oudh da Bakhoor yana karya azumi?

Amsa: Turaren da ba shi da ƙarfi ba ya karya azumi, amma Bakhoor mai tsananin hayaƙi zai iya ɓata azumi idan aka shaƙe shi dayawa har ya shiga ciki. Turare ba ya ɓata azumi.

Mu haɗu a tambaya ta gaba.
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*▫️Ansar.*

*📚Irshadul Ummah.*

Ku kasance da mu a Whatsapp ta wannan number *08166650256.*

Telegram:
https://t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)