YIN AIKI DOMIN ALLAH {1}
Yaku bayin Allah, kusani cewa Allah ba ya karbar aikin bayi sai idan an yi aikin dominsa. Duk wanda ya aikata aiki ya yi tarayya da Allah a cikin wannan aiki, to Allah ya wadatu ga barin karbar wannan aikin, duk kuwa yadda wannan aiki yake da yawa. Allah yana cewa:
( إِنَّا أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ فَاعْبُدِ اللَّهَ مُخْلِصًا لَهُ الدِّينَ 2أَلَا لِلَّهِ الدِّينُ الْخَالِصُ3) [الزمر: ٢ – ٣].
*Haqiqa mun saukar maka da littafi da gaskiya, ka bautawa Allah Shi kadai kana mai tsarkake aiki dominsa. Ku saurara tsarkakakken addini na Allah ne”.*
Hakanan yake cewa:
(قُلْ أَمَرَ رَبِّي بِالْقِسْطِ وَأَقِيمُوا وُجُوهَكُمْ عِنْدَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ29) [الأعراف: 29]
*(Ka ce da su, Ubangijina ya yi umarni da tsayar da adalci. Kuma tsayar da fiskokinku a kowane masallaci. Kuma ku bautawa masa kuna masu tsarkake bauta dominsa).*
Ya kuma cewa a wani wurin:
(فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ14) [غافر: 14]
*(Ku bautawa Allah kuna masu tsarkake addini gare shi, Shi kadai, koda kafirai sun qi).*
Hakanan ya sake cewa:
(هُوَ الْحَيُّ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ فَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ65) [غافر: 65]
*(Shi ne rayayye babu abin bauta da gaskiya sai shi. To ku bauta masa kuna masu tsarkake addini gare shi. Gudiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai).*
Ya sake cewa,
(وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ5) [البينة: 5]
*(Ba a umarce su da komai ba sai su bauta wa Allah suna masu tsarkake addini agare shi. Kuma su tsaida sallah, su ba da zakka, wannan shi ne addinin miqaqqiyar hanya).*
Yin aiki domin Allah shi ne, ka yi aiki domin neman yardar Allah ba ta tare da hada shi da wani ba. Ba riya, ba yi don a ji. Idan aiki ya zama haka, to ya lalace, mai yin aikin ma ya halaka.
*الله تعالى أعلم*
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_