WANDA WUTA TAKE HARAMTA A GARESHI 🔥

🔥 WANDA WUTA TAKE HARAMTA A GARESHI 🔥


🍁 Bayin Allah sukan kasu ne gida biyu a ranar lahira, akwai ahlin wuta, sannan kuma akwai ahlin aljannah, wanda hakan ya danganta da gwargwadon yadda bawa ya mu'amalanci ubangijinsa Allah tun anan gidan duniya.

🍁 Akwai halaye da Allah yake rabawa bayinsa anan duniya, akwai hali nagari sannan kuma akwai hali na banza, Allah yakan baiwa kowa halin da ya dace dashi ne, daga nan sai ya zanto sanadiyyarsa ta shiga aljannah, ko kuma wuta, Ya Allah ka karemu daga wuta. 👏🏻

🌴 An karɓo daga Abdullahi ɗan mas'ud, Allah ya ƙara masa yarda yace: Manzon Allah ﷺ, yace: *"Shin bazan baku labarin wanda yake haramta ga wuta ba, ko wanda wuta take haramta akansa ba?, to shine duk wani makusanci (ga mutãne), mai laushin zuciya, mai sauƙin hali"*
📒 Jami' At-tirmiziy (2488)

*🤲🏻 Ya Allah ka haramta rabonmu a cikin wuta, kuma ka haramta rabonta akanmu a ranar gobe ƙiyamah, Amin.*

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)