HAƊUWA ACI ABINCI SUNNA CE DA AKA MANTA DA ITA



HAƊUWA ACI ABINCI SUNNA CE DA AKA MANTA DA ITA 

Daga Jabir رضي الله عنه yace, Manzon Allah ﷺ yace:-
*(mafi albarka da soyuwar abinci a wajen Allah shine Wanda hannuwan mutane suka yawaita wajen cikin sa)*
@حسنه الألباني، السلسلة الصحيحة (٨٩٥). 

الصنعاني رحمه الله:
Yana cewa:-
*Cin abinci mutane da yawa yana nuna akwai haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin mutane da son juna da zaman lafiya, kuma yana janyo wannan abincin yayi albarka, kuma yana kara soyayya da kaunar juna tsakanin mutane........"*
@التنوير شرح الجامع الصغير (١/٣٩٤)]

Yana cikin hanyar tarbiyantar da yara son junan su da hakuri da juna haɗa masu abinci su ci tare ko da kuwa suna yin faɗa da rigima irin nasu na yara, amma idan mahaifa suka kula da hakan suka dage tare da addu'a har sai yaran sun saba sun daina duk wata riga, sai su tashi da dabi'a son junan su da hakurin zama da juna.

Yazo a cikin littafin Adabul mufrada da sanadi mai kyau, ɗaya daga cikin Manyan sahabban Manzon Allah SAW ya kasance baya cin abinci shi kadai, sai ya nemo wani sun ci tare ko kuwa bawansa ne, sai hakan ya janyo masa kauna da soyayya a wajen mutane.

Hatta Manzon Allah SAW baya cin abinci shi kada6i sai tare da mutane kamar yadda sahabi abi hurairata ruwaito kissar shan madara acikin littafin Riyadua saliheen

   Allah ne mafi sani

Allah ka bamu ikon raya wannan sunnar da koyi da Manzon Manzon Allah SAW a dukkan rayuwar mu baki daya.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)