YIN ISTI'AZA A YAYIN HAMMA BASHI DA ASALI A SUNNAH

YIN ISTI'AZA A YAYIN HAMMA BASHI DA ASALI A SUNNAH
:


*TAMBAYA*❓
:
Salaamun Alaykum warahmatullah.
Allah ya karawa malam lafiya da ilimi da fahimta.

Malam shin menene matsayin fadin istikhaza a yayin da mutum yake hamma a shari'ah?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Faɗin isti'azha ko a'uzhu billahi minash shaiɗanir rajim lokacin da mutum yayi hamma baya da asali ko matsayi a shari'a, ma'ana, Allah ko Manzo bai umarni da haka ballantana ya koyar.

Abin da yake da asali shine, Annabi yace hamma daga shaiɗan ne, don haka idan ɗayan ku ya ji ta, yayi ƙoƙarin gimtse ta idan ta rinjaye shi, toh ya rufe bakin sa da tafin hannun sa

قال النبي ﷺ أن التثاؤب من الشيطان، فإذا تثاءب أحدكم فليكظم ما استطاع،

 عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((إِذَا تَثَاءَبَ أَحَدُكُمْ فَلْيَضَعْ يَدَهُ عَلَى فِيهِ وَلاَ يَعْوِي فَإِنَّ الشَّيْطَانَ يَضْحَكُ مِنْهُ)).

Wannan shine abin da ya inganta ko ya tabbata a shar'ance, da ace faɗin isti'azha ya inganta, toh da a daidai wannan lokacin ne za'a koyar ma musulmi da shi.

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :
 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)