AN YI RINTON SAKI TSAKANIN MATA DA MIJI, MENE NE MAFITA?

AN YI RINTON SAKI TSAKANIN MATA DA MIJI, MENE NE MAFITA?
:


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum malam tambayata ita ce miye hukuncin wannan auren a musulumci? Miji ya ce wa matarsa idan kika je anguwarki  ki dawo karfe 4, idan kika wuce haka a bakin aurenki. To malam sai ta kara minti daya to wai shin saki daya ne ko uku? Shi miji ya ce daya ita kuma ta ce uku tunda a bakin aurenta ya ce. To malam miye mafita?

:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus Salamu, duk lokacin da aka yi saki, sai kalmar da aka yi amfani da ita wurin yin saki ɗin ba ta bayyana saki nawa ake nufu a zahiri ba, to a nan miji ne yake da ikon faɗin ko saki nawa yake nufi ba matar ba, idan kuma duk aka kasa samun daidaito, to sai a garzaya zuwa wurin quliya, domin shi idan ya ba da hukunci dole ne a sallama.

Sannan kuma game da mijin da ya ce wa matarsa idan ta aikata abu kaza a bakin aurenta, sai ko ta aikata ɗin, to irin wannan matsalar malamai sun yi mata kallo ta fuskoki guda biyu, idan miji ya ce wa matarsa haka da nufin ya sake ta ne, to wannan mata ta saku da ijma'in malamai.

Amma idan miji ya ce wa matarsa haka da nufin tsoratar da ita ce da hana ta aikata wannan abin, ba manufarsa sakinta ya yi ba, sai kuma aka yi rashin sa'a ta aikata hakan, to wasu malamai sun ce wannan hukuncinsa shi ne hukuncin kaffarar rantsuwa ba hukuncin saki ba, kamar yadda Shaikh Ibn Baáz ya yi bayani.
Majmú'u Fataáwá na bn  Baáz 22/106.

Saboda haka lamarin saki yana hannun miji ne ba mata ba. Duba amsar tambaya ta 119 don qarin bayani a kan hukuncin wanda ya ce wa matarsa idan ta aikata abu kaza a bakin aurenta.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)