INA SO IN SAN WATANNIN AIKIN HAJJI?

INA SO IN SAN WATANNIN AIKIN HAJJI?


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum warahamatullah, malam dan Allah mutum ne ya yi umarah a watan shawwal to yanzu in mutum zai yi aikin Hajj Tumatu'i Sai ya sake wani umarah? Allah ya ba da ikon amsawa.

:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus Salamu Wa Rahmatullah, ƴar uwa  dama shi aikin Hajji na Tamattu'i malamai sun bayyana shi da cewa: Shi ne mutum ya yi aikin Umra a cikin watannin aikin Hajji, daga bisa ni kuma sai ya dawo ya yi aikin Hajji.

Watan Shauwal yana daga cikin watannin aikin Hajji kamar yadda maz'habobi huɗu na Fiqhu suka tabbar. Tun da haka ne to ashe ba sai kin sake yin wata umra ba, tun da dama Hajjin Tamattu'i shi ne maninyaci ya yi umra a watannin aikin Hajji, daga bisani kuma ya zo ya yi aikin Hajji.

Watanin Aikin Hajji su ne Shauwal, da Zhulqa'ada, da kuma Zhulhijja gaba ɗayansa a Maz'habar Malikiyya. Amma a maz'habar Hanafiyya, da Hanabila, watannin aikin Hajji su ne Shauwal, da Zhulqa'ada da kuma kwanaki goma na farkon Zhulhijja.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)