BANI ARON WAYAR KA
(Gajeren labari ne mai dauke da darasi a cikin sa)
Daga: Kabiru Yusuf Fagge
Muna zazzaune a farfajiyar asibitin muna jiran likitocin, wani a gefe yana ta surutu kamar carki. Jim kaɗan wani da ke gefena ya tashi, ya shiga cikin ofishin likitoci na 4 (consulting room 4) Na yi mamakin shigar shi, don ban ji an kira shi ba. Kamar minti ɗaya sai ga shi ya fito, gadan-gadan ya tunkaro ni rai a ɓace. Yana zuwa ya miƙo min hannu. "Ban aron wayarka." Na noƙe kai. "A'a." Hankalin mutanen da ke wajen ya yo kaina. "Me ya sa?" "Saboda ba na bayar da aronta." "Ai shi ne na ce saboda me?" "Saboda sirrina da tsarona duk suna cikinta." "Ni fa ba hotunanka zan buɗa ba, kira zan yi gida a kawo min wani katina da na manta, sai da shi likita zai ganni." "E duk da haka ba zan bayar ba,"
"Haba bawan Allah kana Musulmi ba zaka taimaka wa ɗan'uwanka Musulmi ba." Mai surutun nan ya tsomo baki. "Musuluncin ne ya ba ni damar in yi takatsantsan kar in zama sha ka-tafi." Mai surutu ya yi tsaki, ya zaro wayarsa wadda ta fi tawa tsada, yana kaɗa ta a hannunsa. "Mu ma Allah Ya hore mana wayar fiye da taka, bari in taimaka masa." Ya miƙa masa. Mutumin ya karɓa. "Na gode kira zan yi 'yan sakannni." Ya daddana lambobi, ya kara a kunne. Na ci gaba da rubutun da nake a wayata mai surutu da waɗanda yake yi wa surutun suka ci gaba da sha'anin gabansu. Mintuna sama da ashirin suka wuce, na ji wajen ya yi tsit. Sai kuma zumbur mai surutun nan ya miƙe.
"Bayin Allah mutumin nan da na arawa waya ina ya yi, ko yana ofis ɗin likita?" Aka duba ba ya cikin ofis ɗin, wasu suka bazama waje, nan ma ba ya nan. Ni kam ina zaune ina yin abin da ke gabana. Mai surutu ya iso kusa da ni.
"Malam ka san wannan mutumin da ya ce ka ara masa waya ɗazu-ɗazun nan?" Na kalle shi. "Da na san shi ba aro zai nema ba, karɓa zai yi ya kira." Ya ɗora hannu a ka. Na ci gaba. "Kai da ka san shi ai ka ba shi taka wayar ko?" "Inna lillahi. Wallahi ban san shi ba." "To lallai ba ka da tsaro bawan Allah, wataƙil ya gudu da wayarka."
Wani a gefe ya amsa da faɗin. "Ai tabbas ya gudu da ita! Abin da ke faruwa a asibitin nan kenan kwanan nan. Haka kawai za ka ga mutum hajaran-majaran shi kaɗai ko su biyu su nemi ka taimaka ka ba su aron waya su kira, kawai sai su gudu da ita. Idan ma ba su gudu da ita ba, to za su ɗebi bayanan yadda za su kwashe kuɗinka na banki..." "Inna lillahi..." Cewar mai surutu. Na kalle shi. "Ba tsayawa za ka yi a nan ba." "To ya zan yi?" "Akwai kuɗi a asusun ajiyarka na banki?" Na tambaye shi. "Da yawa ma, duk jarin Hajiya na kasuwa suna ciki." "To hanzarta ka je, ka rufe layinka ko a yi maka sakiyar da ba ruwa." Ai kuwa abin da ya faru kenan, domin kafin mai surutu ya ɗauki matakin tsaro sun yi masa tatas. Ba waya, babu lalita.
Sai an lura, an yi tsaro gwargwadon iyawa, an yi addu'a sai abubuwan su zo da sauƙi. Allah Ya tsare.
Copied