*💫Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi.*
*✨سؤال وجواب في أحكام الصيام.*
Wallafar:
*Sheikh Muhammad bn Salih Al-Uthaimin.*
.
.
(6) ABUBUWAN DA BA SU KARYA AZUMI.
*4. Sumbatar matarka ko mafarki na sha'awa da rana a watan Ramadan.*
.
Tambaya I: Shin ya halatta mutum mai azumi ya sumbaci matarsa ko ya yi wasa da ita da rana a Ramadan?
Amsa: Ya halatta mutum ya sumbaci matarshi ko ya yi wasa da ita saidai idan yana tsoron fitar da maniyyi. Idan ya fitar da maniyyi, zai kame bakinshi daga ci da sha ko wani abu na sauran yinin kuma wajibi ne ya rama azumin. Idan ba a cikin Ramadan bane kuma azumin na wajibine, azumin ya lalace amma babu bukatar ya kame bakinshi amma dole ya rama azumin. Idan azumin ba na farilla bane, azumin ya karye amma babu buƙatar ya rama azumin.
.
Tambaya II: Shin mafarkin da maniyyi ya fita a yinin Ramadana zai iya shafar azumin mutum?
Amsa: Mafarki ba zai shafi azuminshi ba domin ba zaɓinshi bane. Bugu da ƙari, an ɗauke alƙalami a kan duk wanda yake bacci.
.
.
*5. Gulma da Tsegumi.*
Tambaya: Shin gulma da tsegumi suna ɓata azumi?
Amsa: Tsegumi da gulma ba su karya azumi amma suna rage ladar azumi.
.
Mu haɗu a tambaya ta gaba.
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*▫️Ansar.*
*📚Irshadul Ummah.*
Ku kasance da mu a Whatsapp ta wannan number *08166650256.*
Telegram: