DAMBUN COUSCOUS

*🥘GARKUWA RAMADAN KITCHEN*🥘🥙


            *DAY 3*

*DAMBUN COUSCOUS*

Abubuwan haÉ—awa

1-Cous-cous
2-Alayyahu
3-Attaruhu,Albasa
4-GyaÉ—a
5-Mai
6-Nama
7-Curry
8-Da kalolin maggin da kike amfani dashi.

*YADDA AKE HAÆŠAWA*

_Da farko za ki gyara alayyahun ki ki yanka su manya ki zuba gishiri ki zuba ruwa ya ɗan yi mintuna sai ki wanke ki tsane shi ki ajiye a gefe. Sannan ki jajjaga taruhun ki da albasa dai dai yadda kike son ta fito miki ki daka gyaɗar ki, ki nemi roba mai kyau ki juye kuskus ɗinki sannan ki zuba gyaɗa da kayan miyanki da su curry ki gauraya sai ki ɗauko alayyahun ki ku zuba dama kin silala namanki kin yanka shi ƙanana sai ki juye ki juye albasarki da ɗan dama wanda kika yanka sai ki ɗauko ruwan namanki ki juye a ciki iya shi ya isa ya turara miki ki gauraya har sai ya haɗe jikinsa sannan ki juye a madambacin ki mai kyau ki ɗaura a kan wuta, ki bashi mintuna za kiji yana fitar da ƙamshi sosai sai ki sauƙi ki zuba masa mangyaɗan ki da kika soya in kina so za ki iya zuba masa yajin ƙarago ki gaurawa sai ci._
Aci daɗi lafiya.😋

*Hafsat A Garkuwa*✨🌹
08132761212
Post a Comment (0)