JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 02
Tun farkon duniya muslunci aka sani, da shi Annabi Adam AS ya sauko daga aljanna, sai dai daga baya shedan kamar yadda ya yi alqawarin zai batar da bayi ya yi ta qoqarin hakan har qarfin da addinin yake da shi ya yi rauni, kafurci ya amsa ya fara neman yaqarsa a boye da sarari, sai Allah SW ya aiko Annabi Nuh AS bayan qarni 10 da saukowar Adam AS, jama'arsa suka qaryata shi Allah SW ya halakar da su ya sake ba wa muslunci wannan qarfin na jagoranci, bayani zai zo anan gaba.
.
To daga baya lamuran suka sake tabarbarewa qarfin da musluncin yake da shi ya sake qwacewa, sai turo wani Annabin ya dawo bayansa a koma ruwa har zamanin Annabi SAW, daga lokacinsa zuwa wafatinsa muslunci ya qara qarfin da ya ragargaza Farisa wato Iran, ya bi Rumawa har babban birninsu da ake kira Istambul a yau, ya yi qarfin da ba a magana, yayin da al'umma suka yi rauni sabo ya yi yawa sai lamarin ya sake tabarbarewa har ya kasance komawarta zuwa ga buwayarta irin na da abu ne da bai da sauqi, duk da cewa ba yanke qauna aka yi ba, ga dai matsatsin da aka daura wa muslunci ta ko'ina amma musulmai har yanzu suna tunanin cewa za su iya komawa ga jagoranci koda abokan gaban sun tabbatar da cewa hakan ba mai yuwuwa ba ne.
.
Musulmi ya aminta da alqawarin da Allah ya yi masa na cewa jagorancin duniyannan zai ba da shi ne ga bayinsa na gari, wannan kuwa ba fage ne na qila-wa-qala ba, bare a ce mafarki ne ko burin da musulman suke yi, sakankancewa ce da alqawarin Allah SW. Manyan malamai a fanni daban-daban na ilimi sun firfito da ilimi wanda zai amfanar da wannan al'umma, kamar yadda suka yi sharhi mai tsawo game da raunin ko halin ni-'yasu da muka shiga da jifa kala daban-daban da abokan gabar muslunci suke mana masamman Yahudu da Nasara.
.
Dubi dai yadda Yahudawan suka bullo wa Muslincin ta hanyar gardama kan saqon da Annabi SAW din ya zo da shi, suka yi amfani da wasummu, suka musanta Qur'ani da hadisi, da sahabban Annabi SAW matansa da 'ya'yansa, suka jirkita addinin gaba dayansa ya zamanto mu musulman 'yan uwansu mu ne abokan gabansu na farko, a kullum sai tsine wa Yahudawa suke yi amma fa suna tare da su, ba ka taba jin matsala tsakaninsu sai ta fatar baki, ga shi ana ta yi wa musluncin gibi ta hanyarsu.
.
Su ma nasaran sun sami damar shigo mu a dabarce, suka yi rubuce-rubuce da harshen Larabci, har muka zata littafan da suka sako mana na addini ne, muka saki Qur'ani da hadisi da koyarwar Annabi SAW, muka kama surutansu da rubuce-rubucensu wadanda suka tara masa lada masu dimbin yawa sama da saqon da Annabi SAW ya zo da shi, da haka sai suka ajiye saqon a gefe guda suka riqi malamansu, suka ba su girman da bayanansu suke daidai da saqon da Annabi SAW ya zo da shi, wannan ma babban lahani ne da ya samar mana da wagegiyar baraka tunda su ma a qarshe duk wanda zai tsaya a aqidar Qur'ani da sunna to fa yana yaqi ne da malamansu, ma'ana za su yaqe shi ta kowace irin hanya.
.
Sai dai duk yadda al'umma ta lalace za ka taras addinin Allah SW da sauransa, wannan kam ya yi alkawarin ba shi kariya koda kafurai da munafuqai sun qi, ya bar mana addini a qasa qwara daya tal wato mahaifar Annabi SAW, duk yadda musluncin ya sami matsala a wani wuri za ka taras bai tabuwa anan, sai ya zamanto addinai da aqidun musluncin da suka saba wa tarbiyar Annabi SAW matsalarsu yanzu da wannan qasar ne ko kuma aqidar, Turawa na yaqin aqidar ta waje da duk qarfin da suke da shi, mu kuma muna taimaka musu ta ciki ta hanyar mabambantan aqidun da muka shiga, yanzu kowa matsalarsa qasar Saudiya ta lalace.
.
Abu ne mai matuqar sauqi ka ga mutumin dake qasar Turkiya (wace sai daga baya-bayannan ne ma aka komo da kiran salla da Larabci a qasar ko mace ta sanya hijabi a wuraren aiki) ya yi rubutu mai tsawo kan tabarbarewar qasar Saudiyya, haka qasar Masar duk da lalacewar alamomin addini a can, amma alqalaminsu ya fi kaifi kan tabarbarewar addini a qasar Saudiyya, ko anan Nigeria muna da irinsu, da wahala ka ga rubutu na qarfafa gwiwa a wurin irin wadannan mutanen, kullum sai sacce wa mutane qarfi suke yi, har mutum ya fara ganin to Saudiyannan ma fa ba a kan daidai take ba, ya fahimci cewa yanzu fa kowa dambarwa kawai yake yi.
.
A wannan dan littafi da za mu fara karantawa za mu so mu tuna wa juna yadda musluncin ya faro a jiya, da tabarbarewar da ta riqa samunsu a hanya yana qwatar kansa cikin kariyar mahalicci har zuwa yau dinnan, qila wannan ya ba mu wani haske da za mu fahimci haqiqanin abinda ya dace mu yi, a zahirin gaskiya kisar juna ko a can baya ba ts taba zama mafita ba bare yanzu, haka aibanta juna ta kowani irin yanayi ba mafita ba ne, tsayawa a koyarwar Qur'ani da sunnar Annabi SAW da suka inganta wannan ita ce kawai mafita, duk kuma musulmin Allah ba ya jayayya da wadannan hanyoyi guda biyu, Allah ya sa mu dace.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248