HUKUNCE HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI 5️⃣

HUKUNCE HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI 5️⃣


🔷 Tambaya:- Shin wajibi ne mace mai jego zata zauna ne tsawon kwana arba'in bata sallah bata azumi, ko kuma kawai jinin shine abun lura, da zarar ya ɗauke zatayi tsarki ta cigaba da Sallah?? Sannan meye ƙarancin kwanakin jego??


🔶 Amsa:- Hakika jinin haihuwa bashida wani lokaci ƙayyadadde, aduk lokacin da jinin yake nan zata bar sallah da azumi, mijinta bazai kusanceta ba, amma da zarar ya ɗauke koda bai kai kwana arba'in ba, koda kwana goma ne ko biyar, to zatayi wanka ta cigaba da sallanta da azuminta, sannan mijinta zai iya kusantarta babu laifi akan hakan.
    Almuhim, shi jinin haihuwa abune da yake afili ana ganinsa, aduk lokacin da taga jinin to hukuncin sa na tare da ita, idan ya ɗauke kuma shima hukuncin ya tafi, amma da zai ƙara akan kwana sittin to wannan ya zama na ciwo, kawai zata zauna ne ta daina sallah a iya kwanakin hailarta, idan sun wuce sai tayi wanka ta cigaba da Sallah".

📝 المصدر :
[ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص١١].

# Zaurenfisabilillah 

https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)