*💫Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi.*
*✨سؤال وجواب في أحكام الصيام.*
Wallafar:
*Sheikh Muhammad bn Salih Al-Uthaimin.*
.
.
*(7) AZUMIN MARA LAFIYA, MATAFIYI DA MAI MANTUWA.*
*1. Azumin mara lafiya.*
Tambaya: Mara lafiyan da ba zai iya yin azumi ba, menene ya rataya a wuyarshi?
Amsa: Allah Maɗaukaki Ya ce:
*((فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضاً أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ)).*
Ma'ana: *«To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam.»* Surah Al-Baqarah 2:185.
Yanzu sai mu cewa wannan mara lafiyan, idan ciwon na ɗan wani lokaci ne kuma ya ɓace ya tafi, to wajibi ne a kanshi ya rama azumin da ya sha kafin wani Ramadan ɗin, amma idan ciwo ne wanda ba na warkewa ba, kuma ba a san lokacin warkewarsa ba, a nan, zai ciyar da miskini na kowacce rana, wannan ya ɗauke masa azumin.
.
Mu haɗu a tambaya ta gaba.
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*▫️Ansar.*
*📚Irshadul Ummah.*
Ku kasance da mu a Whatsapp ta wannan number *08166650256.*
Telegram:
https://t.me/irshadulummah1